Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ya mika ragamar mulki ga mataimakin sa Lucky Aiyedatiwa saboda tsananin rashin lafiya da yake fama da shi.
Akeredolu ya aika da wasikar haka ga majalisar dokokin jihar domin ya sanar da su halin da yake ciki.
Akeredolu ya ce zai dawo ranar 6 ga Yuli bayan ya samu sauki sannan kuma ya kammala hutun da yake yi a waje.
Gwamnan ya kwana biyu ba a ganshi ba a ofishin sa, da har aka rika yadawa cewa ya rasu ne ko kuma yana cikin tsananin rashin lafiya.
Gwamnan ya ce zai maida hankali wajen neman lafiyar sa daga yanzu zuwa 6 ga Yuli, lokacin da zai dawo aiki.
Discussion about this post