Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa ta bayyana cewa ta kashe naira biliyan 200 wajen shirye-shiryen fara ƙidayar jama’a da gidaje a ƙasar nan baki ɗaya.
Naira biliyan 200 ɗin da aka kashe dai somin-taɓi ne daga cikin naira biliyan 800 da aka tsara za a kashe kafin kammala ƙidayar.
Shugaban Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), Nasir Kwarra ne ya bayyana kashe kuɗaɗen a wata ganawa da ya yi da shugabannin kafafen yaɗa labarai, ranar Alhamis, a Abuja.
Kwarra ya ce aikin ƙidayar ta hanyar na’urar zamani ya yi tsada ne bisa yin la’akari kayan aikin da ake buƙatar shigowa da su, sai kuma ɗimbin data ɗin da ake buƙata wajen gudanar da aikin ƙidayar.
Ya ƙara da cewa NPC za ta buƙaci ma’aikatan ƙidaya har miliyan 1, domin ganin an gudanar da sahihin ƙidaya kuma karɓaɓɓe a wurin jama’ar faɗin ƙasar nan.
Daga nan ya sha alwashin ganin an gudanar da sahihiyar ƙidaya cikin nasara. Sannan kuma ya roƙi kafafen yaɗa labarai su ci gaba da bayar da ta su gudummawa wajen yayata shirin ƙidayar.
Manajan Ƙidaya Inuwa Jalingo ya ce hukumar ta na aiki ba dare ba rana domin ganin ta cimma kyakkyawar nasarar gudanar da ƙidayar jama’a ta hanyar amfani da na’urar zamani a cikin nasara.
Discussion about this post