Ministan ilimi Adamu Adamu ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa sabbin jami’oi’masu zaman kansu 37, ciki harda karin biya mallakin Farfesa Adamu Gwarzo.
Farfesa Adamu Gwarzo ne ke da mallakin rukunin jam’oin Maryam Abacha dake Kano da Maradi jamhuriyar Nijar.
A cikin jam’oi 37 da gwamnati tarayya ta amince da su ranar Talata, akwai FBI-U dake Kaduna da Kuma Canadian University wacce ta ke a babban birnin tarayya, Abuja. Dukkan su karin jam’o’i ne cikin rukuni jami’o’i dake karkashin Farfesa Adamu Gwarzo.
Minista Adamu ya ce gwamnati ta yi wannan kari ne dubi da dubban dalibai dake gama karatun Sakandare sannan babu isassun guraben ci gaba da karatun jami’a a kasa Najeriya.
” Hakan ya sa dole gwamnati ta ba da daman jam’oi masu zaman kansu su rika samun dama domin yara su samu daman shiga manyan makarantu.
Sai dai kuma minista Adamu bai bayyana sunayen jami’oin ba a lokacin da yake hira da manema labarai.
Shugaban jami’ar MAAUN , farfesa Gwaro ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa yana cike da farin ciki dalilin amincewa da jami’oin sa biyu da gwamnati ta yi da kuma basu lasisin soma aiki.
” Wannan ci gaba ne matuka kuma abin farin ciki ne a gare ni. Babu wani abu da zan yi ko kuma da za mu iya yi domin taimakon dumbin alummar mu musamman talakawa in ba samar wa yara da guraben samun ilimi ba.
” A haka nake kuma buri na shine in ga ana samu cigaba a fannin ilimi a kasar nan da nahiyar Afrika.
Zuwa yanzu akwai jami’oi masu zaman kasu akalla 76 a Najeriya.
Discussion about this post