Salihu Lukman, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Arewa maso Yamma, ya zargi Shugaban APC da Sakataren Jam’iyya, Omisore da ragargazar kuɗaɗen jam’iyya.
Wasiƙar ta Lukman wadda guguwa ta kwaso ta watso a ofishin PREMIUM TIMES, ya rubuta ta a ranar 27 Ga Afrilu, zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari.
Ya shaida wa Buhari cewa ya maka Adamu Sakataren APC na Ƙasa, Iyiola Omisore a Babbar Kotun Tarayya, Abuja.
Haka nan kuma Lukman ya aika wa Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu kwafen wasiƙar, shi da Gwamnonin APC ɗaya bayan ɗaya. Su ma Kwamitin Zartaswar APC ya ce duk ya aika masu da kwafen wasiƙar.
Cikin wasiƙar dai Lukman ya zargi Adamu da Omisore cewa su na kashe kuɗaɗen jam’iyya a ɓoye, su na yin tuwo-na-mai-na su biyu, babu ruwan su da tuntuɓar Kwamitin Zartaswar APC.
Wannan harƙallar da Lukman ya yi zargin su Adamu na aikatawa, ya ce sun karya dokokin jam’iyya.
“Ya Shugaban Ƙasa, ina sanar da kai a cikin ɓacin rai cewa Sanata Adamu Abdullahi da Omisore ba su komai sai take dokar jam’iyya su na karyawa.”
Lukman ya ce Abdullahi Adamu ya ci amanar Buhari, wanda shi ne ya bayar da sunan sa, ya ce a zaɓe shi shugaban jam’iyya.
Ya ce ya bi dukkan hanyoyin da su ka wajaba da waɗanda su ka dace, domin ya saisaita su Adamu, amma abin ya faskara.
Ya ce ganin yadda abin ya ci tura ne dangane da yadda su ke ragargazar kuɗaɗen APC, ya yanke shawarar maka su kotu, tare da sanar da Shugaba Buhari halin da ake ciki.
A ƙarar da Lukman ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/573/2023, ya maka Adamu, Omisore, APC da INEC ƙara.
Ya nemi kotu ta tilasta Adamu ya kira taron Kwamitin Zartaswa, ya bayyana yadda ya kashe kuɗaɗen jam’iyya.
Discussion about this post