Yayin da za a rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, ya kamata Bola Tinubu ya sani cewa Boko Haram ne babban ƙalubalen gwamnatin sa. Bayan an bayyana cewa shi ne ya yi nasara a zaɓen 25 ga Fabrairu, kusan za a ce ya ma fara aikin karɓar mulki, ciki kuwa har da sanar da shi bayanan matsalar tsaro.
A matsayin Tinubu na jagoran APC kuma makusancin Shugaba Muhammadu Buhari, Tinubu zai kuma iya cin ribar samun muhimman bayanai daga zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima. Domin shi ne gwamnan jihar Barno, wadda ita ce jihar da Boko Haram ya fi ragargazawa tun daga 2013 zuwa 2015.
A wancan lokacin sai da Boko Haram su ka ƙwace ƙananan hukumomi 27 a faɗin Arewa maso Gabas. Lamarin da ya haifar da mummunar matsalar ‘yan gudun hijira waɗanda ba dukkan halin ƙuncin rayuwar da su ka shiga ne aka riƙa sani a kafafen yaɗa labarai ba.
Shekaru 14 kenan cur ana fama da Boko Haram, kuma har yau an kasa samun mafita, sai dai har yau amfani da sojoji kaɗai ce hanyar da ake bi. Buhari shi ne shugaban ƙasa na uku da aka yi wanda ya kasa kawo ƙarshen Boko Haram, duk kuwa alƙawarin da ya dauka a lokacin kamfen, shekaru takwas da su ka gabata.
Babban abin damuwa kuma shi ne irin ta’addancin ƙungiyar ISWAP, wadda aka ƙirƙira watanni uku kafin Buhari ya hau mulki cikin 2015. To ISWAP ta yi ƙarfi sosai a zamanin mulkin Buhari. Ta kai manyan hare-hare aƙalla a jihohi bakwai a wajen Barno: Abuja, Edo, Kano, Kogi, Neja, Ondo da Taraba. Kuma duk wurare ne da a can baya ba ta taɓa kai hare-haren ba.
Ba Boko Haram ne kaɗai matsalar tsaro a Najeriya ba. ‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun addabi Arewa maso Yamma, har ta kai mutanen karkara tsawon shekaru da dama su na gudun hijira har zuwa cikin Jamhuriyar Nijar.
Noma ya gagari mutanen karkara. A wasu yankunan ma har haraji su ke ɗora wa jama’ar karkara kafin su ƙyale su su yi noma.
‘Yan bindiga sun haifar da masifar yunwa, hijirar mutanen karkara zuwa cikin birni, asarar rayuka masu yawa da ta ɓimbin dukiya. Al’ummar yankunan karkarar Arewa maso Yamma sai gudu su ke yi, har cikin Nijar, ƙasar da ita ma Boko Haram sun addabe ta.
A tsakiyar Najeriya ana fama da rikici-rikicen makiyaya da manoma. Ga kuma hanƙoron ‘yan neman su ware daga Najeriya a yankunan Kudu maso da kudu maso Kudu.
Ya kamata Tinubu da zaran ya hau mulki, to ya yi gaggawar tabbatar wa duniya cewa zai iya magance waɗannan matsaloli na rashin tsaro.
Kuma zai fara ne daga naɗa shugabannin sassa tsaro waɗanda ya tabbatar za su iya aiwatar da gagarimin aikin daƙile matsalar tsaron da sabon shugaban ƙasa ɗin zai ɗauki amanar aikin ya damƙa masu.