Wasu maza uku sun yi wa wani direban adaidaita sahu fyade a garin Awka dake jihar Anambra.
Wannan abu dai ya auku ne a ranar Litinin din wannan mako.
PREMIUM TIMES ta samu rahoton cewa mazan wanda ake zargin cewa ‘yan yahoo ne sun tsaida da keken adaidaita ya kai su unguwar Okpuno dake Awka.
Da suka isa inda zasu je sai suka umarce shi da ya bisu cikin daki ya karɓi kuɗi bayan a hanya sun yi ta hira da shi. Shigan sa dakin ke da wu ya sai suka danne shi da ƙarfin tsiya suka rika yin karɓa-karɓa da shi suna lalata da shi.
Mazaunan kauyen sun ce ga dukan alamu wadannan mutane sun aikata haka ne saboda su yi wani tsafi da shi.
Kakakin rundunar ‘yan bindiga jihar Tochukwu Ikenga ya tabbatar da aukuwar abin.
Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Echeng Echeng ya ce fannin dake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka ne za ta ci gaba da gudanar da bincike akai.
Ikenga ya ce rundunar ta kama daya daga cikin waɗannan mutane bayan farautar su da suka yi.
“Sakamakon gwajin asibiti ya nuna cewa an yi wa direban fyade amma shi wanda aka kama ya musanta aikata haka.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da farautar sauran mutum biyu din da ake nema domin a hukunta su.
Discussion about this post