Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙara ƙaryata zargin waskewa da maƙudan kuɗaɗen stamp duty da Ɗan Majalisar Tarayya, Gudaji Kazaure ya yi wa wasu hukumomin gwamnatin tarayya.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, ya ce zargin da Kazaure ya yi “ba gaskiya ba ce, bugar da hankulan jama’a ne kawai.”
Tun a ranar Lahadi sai da Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata zargin wasoson naira tiriliyan 89 da Gudaji Kazaure ya yi.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata zargin an dagargaje naira tiriliyan 89 na wasu kuɗaɗen harajin da aka daɗe ana tarawa.
A ranar Juma’a ce Ɗan Majalisar Tarayya Gudaji Kazaure ya yi wannan zargi.
Sai dai kuma washegari a ranar Lahadi, Kakakin Yaɗa Labaran Fadar Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, ya ce wannan zargi na Gudaji Kazaure shafa-labari-shuni ne kawai, ba gaskiya ba ce.
Shehu ya ce ai dokar ƙasa ma ta haramta wani ɗan majalisar tarayya ya yi sakataren kwamitin da manyan jami’an gwamnati ke ciki.
A wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa, Kazaure ya ce shi ne Sakataren Kwamitin Gano Kuɗaɗen Harajin ‘Stamp Duties’, wanda kwamiti ne na Shugaban Ƙasa.
Kazaure ya ce CBN, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, sai kuma Manyan Hadiman Fadar Shugaban Ƙasa sun yi masa katanga, su ka hana shi ganin Shugaban Ƙasa, domin ya yi masa bayanin abin da binciken kwamitin sa ya gano.
Gudaji, wanda ke wakiltar ƙananan hukumomin Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi a Jihar Jigawa, ya ce kwamitin sa ya zargi hukumomi da cibiyoyin gwamnati da laifin yi wa kwamitin sa zagon ƙasa.
Ya ƙara da cewa kwamitin sa ya bankaɗo cewa zunzurutun naira tiriliyan 89 ne aka karkatar, daga kuɗaɗen harajin da bankuna ke cirar wa gwamnati daga masu hulɗa da bankuna, wato stamp duties.
Sai dai kuma Garba Shehu ya maida masa martanin cewa ai tuni aka rushe kwamitin da shi Gudaji Kazaure ya ce shi ne sakataren kwamiti.
Sai dai kuma ya ce akwai kuma wani kwamiti wanda Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya ke shugabanta, wanda aka kafa cikin Juni, 2020, wanda aikin kwamitin shi ne tantance kuɗaɗen harajin ‘stamp duties’ daga asusun ajiyar kuɗaɗe.
“Duk wanda ya san yadda Dokar Najeriya ta ke, ya san ta hana Ɗan Majalisa ya yi sakataren wani kwamiti mai mambobin gwamnatin tarayya a matsayin ‘yan kwamiti.
“Ban san inda ya shafto waɗannan kuɗaɗen da ya ambata har naira tiriliyan 89 ba. Domin ko jari da kadarorin bankunan ƙasar nan ma bai kai naira tiriliyan 50 ba..”
Garba Shehu ya ce Gudaji ai kowa ya san cewa mutumin Shugaban Ƙasa ne, babu mai iya hana shi ganin Shugaban Ƙasa.
Jin yadda Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata shi, sai Kazaure ya fitar da sanarwa ga manema labarai cewa “Shugaba Buhari ne ya kafa kwamitin su, kuma shi kaɗai ke da ikon rushe kwamitin.”
A ranar Talata Garba Shehu ya sake fitar da sanarwa cewa a cikin 2014 lokacin da Buhari ya hau mulki, ya gano cewa akwai wata dokar da ta umarci a riƙa karɓar wasu kuɗaɗen haraji daga hada-hadar kuɗaɗe a bankuna, wato ‘stamp duty’, amma kuma ba a bin dokar ana tara kuɗaɗen yadda ya dace.
“An gano cewa wasu ‘yan harƙalla ne su ka kafa wani garken hamshaƙan masu wawure kuɗaɗen, ta hanyar haɗa baki wasu manyan jami’an hukumar NIPOST, su na karkatar da kuɗaɗen cikin aljifan su.”
“Bayan wata ƙungiya ta nusar da Gwamantin Tarayya cewa Najeriya ta yi asarar naira tiriliyan 20 na Kuɗaɗen hada-hada daga wannan banki zuwa wancan, tsananin 2013 zuwa 2016.
“Wannan ƙungiya ta ce ai za a iya gano kuɗaɗen, a tatso su a maida wa gwamnatin tarayya, jami’an tuntuɓa sun nemi a biya su Naira tiriliyan 1.5, wato kashi 7.5 na kuɗaɗen.
“An amince a haka, kuma aka damƙa kula da aikin na su bisa ƙarƙashin kulawar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
“To ganin yadda aikin ya kakare babu wani ci gaba da aka riƙa samu, a ranar 8 Ga Maris, 2018 sai Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa na lokacin, Abba Kyari, ya rubuta wa ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) cewa a dakatar da aikin zaƙulo kuɗaɗen, tunda babu wani abin a gani a yaba da masu zaƙulo kuɗaɗen zlsu ka yi.”
Daga nan ne Garba Shehu ya ce sai masu aikin zaƙulo kuɗaɗen su ka maka Gwamantin Tarayya kotu, amma gwamnatin ta yi nasara a kan su.
“Daga nan ne kuma sai wannan gwamnatin ta garzaya Majalisar Tarayya ta nemi a yi wa doka garambawul, domin a ɗauke ikon karɓar harajin stamp duty daga hannun NIPOST.
Ya ce daga nan ne sai waɗancan waɗanda aka soke aikin zaƙulo kuɗaɗen daga hannun su, su ka kewaya wajen Gudaji Kazaure, su ka yi masa romon-kunne cewa za su iya zaƙulo kuɗaɗen. A lokacin kuwa Kazaure na sakataren kwamiti. Alhali kuwa tuni wasiƙar Abba Kyari ta tabbatar da rushe kwamitin karɓar kuɗaɗen ‘stamp duty.’ “Daga nan jin cewa ɗan hayar nan ya na kiran kan sa shugaban kwamiti, Gudaji Kazaure kuma Sakataren Kwamiti, sai Buhari ya janye amincewa da kwamitin na su a ƙarƙashin ofishin sa.” Cewar Garba Shehu.