Gwamnan jihar Kaduna ya raɗa wa wasu fitattun gine-gine da titunan jihar sunayen wasu jarumai kuma fitattun ƴan asalin jihar.
Cikin waɗanda aka karrama akwai tsohon mataimakin shugaban kasa, Kuma gwamnan jihar Namadi Sambo, da tsohon mataimakin gwamnan jihar Kaduna Barnabas Bantex.
A hira da yayi kai tsaye da gidajen radiyon jihar ranar Laraba, El-Rufai ya yi haka ne domin saka musu saboda irin gagarimin gudunmawar da suka baiwa jihar.