Gwamnan jihar Kaduna ya yi kira ga ƴan Kaduna da su tabbata sun tambayi duk wani ɗan takara da ke ƙalubakantar gyara aikin malunta da gwamnatin sa ke yi da su faɗi musu irin gyaran da su za su yi da ya fi abinda muke yi.
A hira da yayi da gidajen radiyo a Kaduna ranar Laraba ya ce doka ce suka saka a jihar cewa duk bayan shekaru huɗu zamu sake yin gwajin malaman mu domin inganta su.
” Da muka umarci su su zo a yi musu gwaji a karo ta biyu sai wasu suka ki yi haka kawai wai su ba za su yi ba. Mun sallame su saboda ba su son yin aiki da mu.
” Mu ne muka ɗauke su aiki amma kuma su ce ba za su bi dokar mu ba. Shine ya sa muka sallame su, su kama gaban su.
Gwamna El-Rufai ya ce gwamnatin sa ta maida hankali matuka wajen ganin fannin ilimi ya bunkasa, ƴaƴan talakawa sun samu ilimi cikin sauki sannan kuma tatacce wanda bashi da mis kowacce iri.
” Daga ajin firamare 1 har babban sakandare a Kaduna kyauta ne. Mun gyara shi haka kuma don ƴaƴan talakawa su samu damar karatu.
Discussion about this post