Bayan gobza ya alkalin wasa naushi da shugaban kwallon kafa na Kano Pillars Surajo Jambul yayi a lokacin da ya wasar kungiyar da Dakkada, hukumar kwallon kafa ta kasa LMC ta kori shugaban kungiyar daga halartar wasan Kungiyar kwarakwata sannan ta ci tarar kungiyar naira miliyan 2.7.
Shugaban ƙungiyar Kano Pillars ya fusata bayan kungiyar Dakkada ta farke cin da pillar ke mata a wasan da suka buga, daga nan sai Jambul ya fusata yayi tsalle ya gobza wa alkalin wasa dake gefen fili naushi a haɓar sa.
Bayan haka za a mika Suraj ga hukuma domin a hukunta shi.
Alkalin wasan da Jambul ya gobza wa naushi Daramola Olalekan na tsaye ne yana kallon wasa a daidai Dakkada ta farke cin da Pillar ke mata sai ya ji saukar ƙulli a haɓar sa.
Bayan haka LMC ta ce duk lokacin da Pillar ta sake irin haka za a rika cire mata maki biyu daga cikin makin ta.
Idan ba a manta ba watanni uku da suka wuce an hana Pillars wasa a filin ta na Sani Abacha saboda ragaraga da ƴan kallo suka yi wa motar ƴan kwallon Katsina United.
An ci taran Pillars naira miliyan 9 sannan an cire mata maki uku a cikin makin da ta tara a kakan wasanni na bana, bayan dakatar da Kungiyar daga buga wasa a filin Sani Abacha da aka yi.
Discussion about this post