Ministan Sadarwa Isa Pantami a ranar Lahadi ya kai ziyarar ta’aziya Kano gidan su Hanifa Abubakar, yarinya ‘yar shekara biyar wanda malaminta yayi mata kisan gilla
Pantami, ya wallafa hakan ne a shafinsa na Facebook tare da wallafa hotonansa yana yin ta’aziyya ga mahaifin yarinyar, Malam Abubakar.
Daga bisane, mahaifin yarinyar ya jagoranci shiga cikin gida in da ya yi ma mahaifiyar da yan’uwanta ta’aziyya da nasihohi, a cewar sanarwar.
“Malam Ya yi nasiha ga iyayen yarinya mai albarka, akan wajibcin hakuri lokacin jarrabawa mai tsanani irin wannan.
“Ya roki Allah Ya sanya Marigayiya Hanifa Abubakar ta zama mai ceto a lahira ga iyayenta, Ya kuma bawa iyayen hakuri akan wannan babban rashi da ya faru sanadiyar wasu azzalumai da suka nuna rashin imani.
“Iyayen sun yi godiya ga Malam da adduar fatan alheri akan nasihohi da addu’o’i da ya gabatar. Allah Ya kiyaye na gaba” In ji Pantami.