Babban Daraktan NYSC na Ƙasa, Burgediya Janar Shu’aubu Ibrahim, ya jinjina wa dukkan ‘yan bautar ƙasa waɗanda su ka nuna kishin ƙasar su, suka shiga aikin zaɓen gwamnan jihar Anambra.
Da ya ke yaba masu bayan ya yi rangadin ƙananan hukumomi 9 don ganin yadda ‘yan NYSC ke gudanar da aikin zaɓe, Ibrahim ya ce, “a yau muna alfahari da ku, domin sunan ku ya shiga cikin tarihin waɗanda su ka bayar da gudunmawar tabbatar da zaɓe lami lafiya a Jihar Anambra.”
Shugaban na NYSC ya kuma yaba da irin matakan tsaron da ya ga an ɗauka a mazaɓu da rumfunan da ya ziyarta.
Bayanin sa na cikin wata sanarwa da Hukumar NYSC ta fitar da yammacin Asabar ɗin nan.
Discussion about this post