Gidauniyar ‘Helpline’ dake Abuja ta bayyana cewa aikata abin kunya da ma’aurata ke yi da kuma kyamatar juna ne kan haddasa kashi 75 bisa 100 na mutuwar aure a Najeriya,
Shugaban gidauniyar Dr Jumai Ahmadu ta fadi haka ranar Alhamis a taron tattauna yadda tsanantawa na al’adu, kabilanci da addini ya zama dalili da ke sa ake samun rashin jituwa tsakanin ma’aurata da yakan kai ga har a rabu dole.
” Duk lokacin da aka ce ma’aurata za su rika zama a gida tare amma kuma kowa yana bin wata akida tasa na addine ko kuma al’ada, za a rika samun bambamcin ra’ayi ba kuma za a samu zaman lafiya a wannan gida ba.
Sannan kuma da wasu abubuwa da alada ke hanawa da ko kuma ya sa ma’aurata su yi, shima yakan sa aure ya yamutse kowa ya kama gaban shi.
Dole ma’aurata su jingine banbanci na al’ada da ke tsakanin su, su rungumi soyayyar da ta hada su idan suna so su zauna lafiya a gidan auren su.
” Banbancin addini da al’ada ya zama abin tashin hankali yanzu a gidajen aure yanzu. Shine ke kashe kashe 75 cikin 100 na aurarraki a kasar nan. Ba a samun jituwa daga nan sa a rabu.
A karshe kungiyar ta hori ma’aurata su rika hakuri da juna sannan su jingine al’ada da duk wani abu da zai tarwatsa zamantakewar su a gidan aure. Su tuna cewa soyaya ce ta hada su ba su zo zaman gaba ko tashin hankali ba.
Discussion about this post