Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta ƙwace ilahirin kuɗaɗe da kadarorin gidaje da motocin da katafaren ɗan damfara Obinwanne Okeke ya mallaka a Najeriya.
Zaman yanzu dai Okeke na can kulle a Amerika ya na zaman kurkukun shekaru 10, bayan da aka same shi da laifin damfarar mutane har dala miliyan 11 a Amurka.
Mai Shari’a Peter Lifu ne ya bada umarnin ga EFCC, bayan da lauyan EFCC ɗin mai suna Chinenye Okezie ya roƙi kotu ta ƙwace kadarorin.
Daga cikin kadarorin da aka ƙwace akwai waɗanda su ka haɗa da:
Gida mai lamba 4 da ke Rukunin Gidajen Oakville, Kado Kuchi, Abuja.
Haka kuma an ƙwace duk wani kayan al’atun da ke cikin gidan.
Akwai kuma gida mai ɗakuna 5 a Rukunin Gidajen Standard Estate, Kabusa, Abuja.
Shi ma wannan gida an haɗa da dukkan kayan alatun da ke cikin sa duk an karɓe.
An kuma ƙwace wasu motocin alfarma masu tsada na sa guda biyu, ƙirar Toyota.
“Dama kuma ya miƙa wa Gwamnatin Tarayya Naira miliyan 280, sai wasu Naira miliyan 240 da kuma Naira miliyan 40.
Lauyan EFCC ya shaida wa kotu cewa za a sayar da gidajen a haɗa da kuɗaɗen duk a biya waɗanda ya damfara a Amurka.
Discussion about this post