Juliana Achimugu talaka ce da ke zaune ciki Ƙaramar Hukumar Wushishi a Jihar Neja. Ta tashi iyayen ta ba su gaji komai ba sai noma. Ta shiga harkar noma ita ma, ganin cewa ta nan ne kaɗai za ta iya taimaka wa mijin ta wajen gaganiyar ciyar da iyali. Sai da ta yi zurfi a lamarin ta gano ashe gaskiya ne da Bahaushe ke cewa ‘noma tushen arziki’.
“A yankin da na ta shi nan a Wushishi, noma shi ne sana’ar mutanen mu. Ni ma sai na shiga aikin noma domin ta nan zan iya taimaka wa miji na kuma a riƙa samun ƙarin kuɗaɗen rufa wa juna asiri.
“Na fara ƙaruwa da dabarun noma a lokacin da na samu horaswa daga wata ƙungiya Alluvial Agriculture. Daga nan sai na ƙara zage damtse wajen karɓar aron gonaki.
“Karɓar aron gona akwai tsada a yankin Wushishi. Da ya ke ba ƙarfin aljihu na ke da shi ba. Kadada 1 na ke nomawa. Amma bayan haɗuwa ta da Alluvial Agriculture, sai na ƙara karɓar rabin kadada, saboda na ƙara gogewa da dabarun noma.
“Sannan kuma na haɗu da masu sayar mana da irin shukawa na shinkafa da masara, wato kamfanin Barin and Hammers. A wurin su na ke sayen iri da takin zamani.
“Na kan samu taki samfurin ‘urea’buhu biyu, sai NPK kuma buhu huɗu.”
Ta shaida wa wakilin mu cewa a gaskiya ba ta fuskantar matsalar tsaro, saboda wasu dalilai.
“Ka ga dai inda ake da matsalar tsaron nan, can ne tsallaken kogi, ba a nan ba. Mu kuma ba mu iya zuwa can mu yi noma, duk da arha takyaf da ake karɓar aron gonaki a can.
“Tilas mu ke haƙura a nan tsallaken mu inda gonaki ke tsada idan an je karɓar aro.”
Achimugu ta shaida wa wakilin m cewa ta na cikin wata ƙungiya mai suna ‘Tanku Arewa Farmers Group’.
“Babban amfani da hanyar cin moriyar wannan ƙungiya, shi ne a duk lokacin da biyan lebura kuɗin noma ya yi tsada, sai mu taru a yau mu ɗunguma zuwa gonar mace ɗaya, mu nome gonar ta tas. Gobe kuma sai mu ɗunguma zuwa gonar wata.
“To wannan taimakekeniya ta na zama alheri a gare mu sosai.”
Discussion about this post