‘Yan bindiga sun kashe Soja daya, sun sace malamin jami’a, matar aure da yara 8 a Zariya, jihar Kaduna

0

‘Yan bindiga sun sace malamin jami’ar jihar Kaduna Ahmed Buba a zariya tare da ‘ya’yan sa shida ranar Litinin.

Bayan haka sun harbi wani Soja mai suna Ebuka Okechukwu, wanda ya rasu a asibiti saboda raunukan da ya samu a jikin sa.

Sannan kuma ‘yan bindiga sun shiga gidan makwabcin Buba suka sace matarsa Rabi Isya, da ‘ya’yan ta biyu.

Sai dai kuma ba su yi nisa ba jami’an tsaro suka diran musu. Amma kuma saboda karfin makamai da suka zo da shi sur arce wa jami’an tsaro amma kuma an ceto yara shida cikin 8 din da suka sace.

Wani mazaunin garin Haruna shika ya ce an ceto yaran a unguwar Kasuwan Da’a dake Karamar hukumar Zariya. Ya ce maharan sun kai mutum 30 dauke da manyan bindigogi.

Share.

game da Author