‘Yan sandan babban birnin tarayya sun bayyana cewa sun kama ‘yan shi’a 57 cikin wadanda suka yi arangama da sua a Abuja.
Shugaban wannan tafiya na ‘yan shi’a ya karyata cewa wai mabiyan sun kai wa ‘yan sanda hari a lokacin da suke tattaki domin murnar zagayowar ranar Arbabeen a Abuja.
” Mun so mu yi tattakin mu ne a Mararaba, dake jihar Nasarawa amma kuma da muka ga tarin jami’an tsaron ko ta kwana da aka jibge mana sai muka canja shawara muka garzayo Abuja.
” A Abujan ma can wuraren Gwarinpa muka tafi, muka yi tattakin mu, A daidai za mu yi sallama da juna sai ;yan sanda suka diro mana. Sun kashe mana mutane 8 bayan raunuka da suka ji ma wasu da dama.
” Mu fa wannan tattaki da muke yi muna yin shi domin yin alhinin kisan Sayyidina Hussain da aka yi shekaru da dama a Karbala, shine muke yin tattaki domin nuna rashin jin dadin abin da aka yi wa iyalan manzon Allah SAW.
Ya ce shekaru 40 kenan suna irin haka ba tun yau ba a Zaria. Amma bayan gwamnati ta rusa ginin hedikwatar su ya sa ba su yi a nan.
Yan sanda sun ce wannan tattaki neman magana ce kawai da tsokanan. Sun kama maza 37 mata 18 cikin wanda suka kicime da ‘yan sanda a Abuja.