‘ALO TSIYA ALO DANJA’: Yari ya yi fatali da sanarwar sake rajistar mambobin APC a Zamfara

0

Yayin da ‘yan bindiga ke ci gaba da kisa da garkuwa da mutane da kuma kwasar dukiyar talakawan karkara a Jihar Zamfara, su kuma masu mulki da ‘yan siyasa na jihar a ƙarƙashin APC, sun maida hankali wajen turnuƙun siyasa, wanda a kullum sai ƙara ƙazancewa da dagulewa ya ke yi.

Rikicin baya-bayan nan shi ne wanda tsohon Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari ya yi kira ga magoya bayan sa cewa su yi fatali da umarnin da Gwamna Bello Matawalle ya bayar na sake rajistar mambobin jam’iyyar APC na jihar baki ɗaya, kuma ya ce a sake sabuwar rajista.

Sakataren Ɓangaren Yari na APC, Sani Musa ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Juma’a, a Gusau.

Ya ce tsohon karin shaidar zama ɗan jam’iyyar APC na Zamfara na nan daram.

Uwar jam’iyya ta ƙasa dai ta ƙara wa Jihar Zamfara wa’adin ci gaba da yin rajistar mambobin APC na jihar ne bayan komawar Gwamna Matawalle APC shi da tawagar sa.

An yi haka ne domin a bai wa dandazon ‘yan PDP ɗin da su ka bi Matawalle cikin APC su yi rajista a cikin jam’iyyar.

“Mu na sanar da cewa jagoran mu tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari ya sha faɗa cewa rajistar da mu ka sabunta kafin wasu su dawo cikin jam’iyyar mu a haɗe, ta na nan a matsayin halastacciyar rajista.” Inji sanarwar.

Musa ya bayyana ci gaba da rajistar da ake yi na mambobin APC a Jihar Zamfara a yanzu, karyawa ce da bijire wa umarnin kotu.

“Karya wannan umarni kuma zai kawo wa jam’iyyar tarnaƙi wajen yin nasara a zaɓen 2023 a Zamfara.

Ya ce iƙirari da sanarwar da tsohon Gwamna Yariman Bakura ya yi cewa an soke tsoffin rajistar da aka yi kafin a haɗe, babban kuskure ne Yarima ya tafka, da gangan domin haddasa ruɗu da rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyya.

Musa ya ce bai halasta ba a dokance a ci gaba da yi wa mambobin APC rajista a Zamfara a halin yanzu.

“Ci gaba da rajistar ‘yan jam’iyyar APC a Zamfara da ake yi a yanzu, haramtacce ne kuma zai ƙara rarraba kawunan jam’iyya tare da rasa mulki a zaɓen 2023.

“Mu na jan hankalin mambobin mu da su ka kai mutum 775 cewa tunda sun rigaya sun yi rajista ko sabunta rajista a farko, to su yi watsi da labarin soke rajistar kawai. Kada su sake yin wata rajistar zama mambobin APC kuma.

“Saboda bai yiwuwa mamba ya yi rajista sau biyu.”

Share.

game da Author