A karo na biyar, Gwamnatin Tarayya ta kara wa’adin ranar rufe rajistar hada layin waya da lambar katin shaidar dan kasa zuwa ranar 30 Ga Yuni, wato tsawon watanni biyu nan gaba.
Sanarwar karin wa’adin na cikin wata sanarwar manema labarai da Kakakin Yada Labarai na Hukumar Sadarwa ta Kasa, NCC, Ikechukwu Ayinde da Kakakin Yada Labarai na Hukumar Samar da Katin Dan Kasa, NIMC, Kayode Adegoke su ka sa wa hannu.
Sanarwar ta ce Ministan Sadarwa Isa Pantami ne da kan sa ya sanar da karin na makonni takwas.
Pantami ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi karin ne domin ‘yan kasar nan da mazauna kasar su samu damar mallakar lambar katin shaidar NIN.
Wadanda su ka halarci ganawar sun hada da Minista Pantami, Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa, Adeolu Akande, Babban Shugaban NCC Umar Dambatta, sai kuma Babban Daraktan NIMC, Aliyu Azeez.
Sanarwar ta ce zuwa yanzu an yi wa layukan waya miliyan 190 rajista. Kuma akalla mutum miliyan 54 kenan su ka hada layukan wayar su da lambar katin shaidar dan kasa, saboda an amince mutum ya hada lambobin wayar sa uku zuwa hudu da lambar katin shaidar dan kasar sa (NIN).
Za’a iya hada lambobin waya 7 da lambar katin zama dan kasa 1
Ministan Sadarwa Isah Pantami ya bayyana cewa za a iya hada layukan waya dabam-dabam har bakwai da lambar katin zama dan kasa guda daya.
Isah pantami ya fadi haka ne a lokacin ta ya amsa tambayoyi a wani shirin gidan talbijin din Channels dake Abuja.
” Mun kirkiro manhaja da za ka iya hada layuka bakwai da lambarka na katin zama dan kasa nan take cikin sauki. Mun yi haka ne domin a samu saukin hada layukan ba tare da an wahala.
” Sai dai kuma idan aka sake saka dokar ‘Kulle’ a kasar nan, dole kuma jami’an hukuma NIMC da sauran masu ruwa da tsaki a harkar su koma kan teburin a sake sabon lale, ta yadda za a samu nasarar aikin da aka saka a gaba.
” Idan har aka saka dokar ‘garkame mutane’ dole mu bi doka domin muma ‘yan kasa ne. Saboda haka idan gwamnatin tarayya ta sake saka dokar ta baci, ta umarci kowa ya koma gida ya zauna, dole muma mu canja tsari da lissafin mu.
Hukumar NIN ta gargadi kowani dan kasa ya je yayi rajistan kansa domin samin lambar zama dan kasa kuma ya hada layin sa da lambar kafin 9 ga Faburairu.