Sakamakon bincike da aka yi ya nuna cewa mutum miliyan 1.9 ne ke dauke da cutar Kanjamau a Najeriya.
An gano haka ne duk da namijin kokarin da gwamnati ke yi wajen ganin ta dakile yaduwar cutar a kasar nan.
A jihar Ondo bincike ya nuna cewa mata masu ciki 124,817 na dauke da cutar.
Wannan sakamako ya fito daga gwajin cutar da aka yi a kananan hukumomin dake jihar.
Sakatariyar gwamnatin jihar Oladunni Odu ta fadi haka a taron tattauna hanyoyi dakile yaduwar Kanjamau da aka yi a garin Akure a makon jiya.
Kungiyar ‘APIN Public Health Initiatives’, hukumar CDC Nigeria da gwamnatin Amurka ne suka shirya wannan taron.
Oladunni ta ce gwamnati a shirye take wajen ganin ta dauki matakan da za su taimaka mata wajen dakile yaduwar cutar. Sannan ta yi kira ga masu ruwa da tsaki, sarakunan gargajiya da malaman addini su hada hannu da gwamnati wajen ganin an dakile yaduwar Kanjamau a jihar.
A jawabin ta a wajen taron Jami’ar gwamnatin kasar Amurka Claire Pierangelo ta ce Kanjamau na daya daga cikin cututtukan dake kisan mutane a duniya.
Claire ta ce zuwa yanzu mutum miliyan 38 ne ke dauke da cutar a duniya kuma a shekarar 2019 cutar ta yi ajalin mutum 700,000 a duniya.
Ta ce a Najeriya mutum miliyan 1.9 ke dauke da cutar kuma a shekarar 2019 mutum 44,000 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.
A karshe, Claire ta yi kira ga gwamnati da ta saka dokar hana asibitoci karbar kudade daga hannun masu fama da cutar a jihar.