Yadda barawo ya sace kudin sadakin Naira 100,000 daga aljihun waliyyin amarya a Masallacin Al Noor, Abuja

0

Wadanda su ka halarci Sallar Juma’a da kuma daurin aure a ranar 29 Ga Janairu, 2021, a Masallacin Al Noor da ke Abuja, sun ga abin mamaki da kuma tantagaryar rashin kunya.

Wani barawo ne aka kama ya zura hannu ya sace sadakin Naira 100,000 da aka damka wa daya daga cikin waliyyan amaryar da aka daura wa aure a lokacin, a cikin Masallacin, wanda Ministan Sadarwa Isa Pantami ke karatu a ciki.

Ganau din yadda al’amarin ya faru, ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa bayan Sallar Juma’a aka yi sanarwar daurin auren.

Barawon ya matsa har kusa da da’irar malamai da iyayen amarya, inda jim kadan bayan an damka wa waliyyin amarya sadakin naira 100,000 cif, ya na shafa aljuhun sa kawai sai ya ji kudi ko sama ko kasa.

Nan da nan aka yi cacikui aka damke wanda ake zargin, kuma aka samu kudin a aljihun sa.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da barawon ya ci dukan tsiya, bayan an tube shi, kuma jami’an tsaro su ka buga masa ankwa.

Sai dai bincike ya kara tabbatar da cewa an sake shi daga baya, ba a zarce da shi ofishin ‘yan sanda Wuse 2 ba.

Wani bincike ya kara tabbatar da cewa wannan ke karo na biyu da aka taba sace kudin sadaki a Masallacin An Noor, Abuja, masallacin da Minista Pantami ke karatu.

“Satar sadakin farko da aka taba yi dai an sace kudin tun kafin a daura auren. Hakan ta sa tilas sai dai aka daura auren bisa sharadin bashi aka daura sadaki, kuma za a biya. Sai daga baya angon ya sake samun kudi ya biya.”

Majiya a cikin jami’an tsaron Masallacin An Noor da wadanda aka kama barawon a gaban su, sun roki a sakaya sunan angon da aka sace wa sadakin auren sa, kuma a sakaya sunan waliyyin amaryar da barawo ya saci naira 100,000 na sadakin ‘yar sa a cikin aljihun sa, saboda wasu dalilai.

Masallacin Al Noor ya sha fama da korafe-korafen yawan satar takalma, kamar yadda ake yawan yi a wasu masallatai da dama.

Wani jami’in da ya ce a boye sunan sa ya ce an saki barawon bayan ya nuna nadamar abin da ya yi, kuma ya tuba, tare da alkawarin ba zai kara yin sata ba.

Wannan masallaci ne manyan shugabanni da ‘yan siyasa su ka fi halarta gudanar sa Sallar Juma’a, shi da Babban Masallacin Abuja.

Share.

game da Author