Yadda shugabannin Najeriya karkatar da kudade waje da sunan tura ‘ya’yan su karatu Ingila

0

Wata cibiya mai suna Gidauniyar Zaman Lafiya ta Carnegie Endowment for International Peace da ke Amurka, ta zargi shugabannin da manyan Najeriya cewa su na amfani da makarantun Birtaniya su na karkatar da kudaden gwamnati da su ke sata su na kai wa waje, sun a karantar da ‘ya’yan su ilmi mai tsada da kudin jama’a.

Wannan bayani ya na kunshe a cikin wani rahoto da aka fitar a Washington DC a ranar Alhamis.

Bayanin ya tabo yadda manyan shugabanni da ‘yan siyasa ke kashe kudade a makarantun Ingila.

Marubucin rahoton mai suna Methew Page, masanin harkokin Najeriya ne ciki da baya, musamman harkokin tsaro da leken asirin Najeriya, inda ya rika yin ayyuka na jami’an tuntuba.

Sannan kuma Gwamnatin Birtaniya ce ta dauki nauyin buga rahoton, kamar yadda Catriona Laing ta bayyana a ranar Juma’a a Abuja.

Rahoton Carnegie ya nuna tabbas wasu makarantun na Birtaniya na da hannu cikin harkallar, wato da masaniyar kuma da hadin kan su ake wannan cuwa-cuwa.

Sannan kuma rahoton ya zargi Gwamnatin Birtaniya da ‘‘gudanar da tsarin ilmi wanda ke bada kofa ana cuwa-cuwa da harkalla a tsarin ilmin kasar.’’

Rahoton ya kara cewa makarantun kasashen Turai ta Yamma sun taimaka wajen daure wa shugabannin wasu kananan kasashe su na wofintar da muhimmancin ilmi a kasashen su na haihuwa.

Gidauniyar ta zargi shugabannin da manyan Najeriya cewa su na amfani da makarantun Birtaniya su na karkatar da kudaden gwamnati da su ke sata su na kai wa waje, su na karantar da ‘ya’yan su ilmi mai tsada da kudin jama’a.

Wannan bayani ya na kunshe a cikin wani rahoto da aka fitar a Washington DC a ranar Alhamis.

Bayanin ya tabo yadda manyan shugabanni da ‘yan siyasa ke kashe kudade a makarantun Ingila.

Marubucin rahoton mai suna Methew Page, masanin harkokin Najeriya ne ciki da baya, musamman harkokin tsaro da leken asirin Najeriya, inda ya rika yin ayyukan jami’an tuntuba.

Rahoton ya kara cewa makarantun kasashen Turai ta Yamma sun taimaka wajen daure wa shugabannin wasu kananan kasashe sun a wofintar da muhimmancin ilmi a kasashen su na haihuwa.

Share.

game da Author