An bayyana zargin cin hanci da rashin alkibla da rashawa a shirin raba agajin kudi ga mata marasa galihu a Ma’aikatar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa cewa duk karya ce kawai.
Minista Sadiya Farouq ta karyata wani labari da aka bayar inda aka ce wai akwai cin hanci da rashawa da kuma rashin alkibla a shirin ma’aikatar ta na raba agajin kudi ga mata marasa galihu.
A cikin wata sanarwa da ta rattaba wa hannu a cikin wannan makon, ministar ta ce labarin wata jarida ta buga a ranar Lahadi, 24 ga Janairu, 2021 inda aka yi wannan ikirarin duk zuki-ta-malle ce da rashin fahimtar hakikanin manufar shirin.
Ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta fito da shirin na ‘Household Uplifting Programme-Conditional Cash Transfer (HUP-CCT)’ a shekarar 2016 ne tare da hadin gwiwar Bankin Duniya da nufin samar da kariya daga fatara ga mabukata a Nijeriya.
“Hakan ya yi daidai da shirin gwamnatin Shugaba Buhari na inganta rayuwa tare da yakar fatara da yunwa a cikin al’umma,” inji ta.
Sadiya ta ce a shirin ana biyan kudi N5,000 ne ga gidajen fakirai wadanda yawanci a yankunan karkara su ke.
Mijistar ta bayyana cewa shirin ya na da wasu manufofi da su ka hada da: inganta abincin da ake ci a cikin gidaje tare da gyara yanayin tattalin arzikin jama’a; kara yawan hanyoyin inganta kiwon lafiya da abinci; inganta shigar yara makaranta da ci gaba da karatun su;inganta kiwon lafiya a tsakanin al’umma.
Akwai kuma inganta hanyoyin samun kudi da kayan ayyukan yau da kullum da kuma inganta tattalin arzikin iyali da rage musu fatara.
Sai rungumar masu cin moriyar shirin tare da kuma hanyoyin samun abincin su.
Ministar ta ce gaba daya ma dai shi wannan shiri wani bangare ne na kudirin gwamnati na rage fatara a cikin al’umma a Nijeriya.
Yayin da ta ke bada jadawalin nasarar da shirin ya samu, Hajiya Sadiya ta ce ya zuwa watan Disamba na 2020, an gudanar da shirin a jihohi 33 na kasar nan har da Yankin Babban Birnin Tarayya. Sannan an samu jimillar mutum 1,414,983 da su ka ci moriyar shirin da gidaje 7,068,629 da aka shigar cikin shirin, wanda ya shafi Kananan Hukumomi 487, unguwannin mazabu 4,716 da kuma kauyuka 37,628.
A cewar ta, shirin na da burin ya isa kowace jiha ya zuwa watan Maris, 2021.
Ta ce, “Akasin ikirarin da aka yi na cewar wai shirin bai da tsarin gudanarwa, a gaskiya wannan shiri ya na da kyakkyawan tsarin aiwatarwa tare da hanyoyi a rubuce a komfuta kan yadda ake rubuta sunayen duk wadanda su ke cin moriyar sa, wanda ya ginu a kan gidajen fakirai ko marasa galihu wadanda ake samo bayanan su daga Rajistar Jama’ar Kasa, wato ‘National Social Register’.
Sadiya ta ce, “Ana samun irin wadannan mutane ne ta hanyar tsarin bincike da tambayar jama’a wanda sashen jami’ai masu kula da kowace jiha da mu ke da su, wato ‘State Operating and Coordinating Units (SOCU)’ a karkashin kulawar ofishin mu mai kula da binciko hanyoyin yaki da fatara na kasa, wato ‘National Social Safety Net Co-ordination Office’ (NASSCO) su ke yi.
Discussion about this post