Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bayyana cewa sallamar kociyanta da ta yi ya zama dole ganin yadda kungiyar kwallon kafar ke tangal-tangal a kakar wasan kwallo na wannan shekara na Premier League.
Duk da cewa Chelsea ta yi nasara a wasan FA Cup da ta buga da Luton ranar Lahadi, kungiyar ta ce Lampard ya gaza matuka a wasannin da yake bugawa na Premier League.
Kungiyar ta ce shawarar sallamar Lampard shawara ce mai wahalar gaske amma dole ta yi haka domin ci gaban kungiyar.
“Muna godiya ga lampard bisa nasarorin a kungiyar tare da ‘yan wasan kungiyar. Idan da so samu ne da mun barshi ya ci gaba da koyar da ‘yan wasan amma hakan ba zai yiwu ba ganin yadda a kullum jiya iyau.
Haka nan shima mai kungiyar kwallon kafan ya Abrahamovic, ya jinjina wa Lampard sannan ya kara da cewa ba zai taba mantawa da gudunmawar da ya ba kungiyar ba a lokacin yana dan wasa da kuma zaman sa da yayi na Kochiyan kungiyar.