Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump ya tabbatar da cewa ba zai halarci bikin karbar mulki daga hannun sa a damka wa zababben shugaban kasa Joseph Biden ba.
“ Ga amsa zuwa ga masu yawan tambaya. To ba zan halarci bikin damka wa mulki ga sabon Shugaban Kasa ba, a ranar 20 Ga Janairu, 2021.” Haka Trump ya bayyana a ranar Juma’a, kafin a kulle shafin sa na Twitter, Facebook da Instagram.
Yanke shawarar da ya yi cewa ba zai halarta ba, ta zo ne makonni da dama bayan ya yi amincewa ya sha kaye a zaben da aka bayyana Biden ne ya yi nasara.
An dai gudanar da zaben a ranar Ga Nuwamba, 2020.
Sai dai kuma daga baya a ranar Alhamis da ta gabata, Trump ya amince ann kayar da shi, inda ya bayyana cewa wata sabuwar gwamnati za ta kama mulki bayan saurkar sa.
Ya kara da cewa zai bada mulki salum-alum.
Biden dai idan aka rantsar da shi, zai kasance Shugaban Amurka na 46.
Ya tabbata ya yi nasarar lashe zaben bayan da Majalisar Amurka ta jaddada nasarar sa ranar Alhamis.
An tabbatar da Biden duk kuwa da shigar-kutsen da ‘yan jagaliyar Trump su ka yi tare da hargitsa zaman majalisar.
Biden ya ci zabe da kujeru 306, shi kuma Trump ya samu 232.
Rabon da wani shugaban Amurka ya kaurace wa mika wa wanda ya kayar da shi mulki, tun cikin 1921, inda Shugaba Woodrow Wilson ya kasa halartar damka wa Warren Harding mulki, saboda matsalar rashin lafiya.