Ba Shugaban Bankin FCMB ne ya yi cikin ’ya’ya na biyu ba – Moyo, matar Thomas

0

Matar da ake zargin cewa Shugaban Bankin FCMB, Adam Nuru ya haifi yara biyu tare da ita, ta fito ta yi magana, mako daya bayan fallasa wannan bahallatsa a ranar 1 Ga Disamba, 2021.

Bahallatsar, wadda tuni ta yi sanadiyyar dakatar da Nuru daga shugabancin FCMB, ta kai ga matar mai suna Moyo Thomas fitowa fili ta karyata zargin da ake yi mata.

Baya ga zargin ta da haihuwar yara biyu tare da Adam Nuru, an kuma yi zargin cewa wannan bakin cikin ne ya yi sanadiyyar ajalin mijin ta, Thomas, wanda shi ma ma’aikaci ne a FCMB din.

Moyo ta bayyana cewa ko da wasa ba ta taba kiran mijin ta Thomas a waya wai ta shaida masa cewa ba shi ne ya yi mata cikin yaran su biyu ba.

“Tunde shi ne uban yara na biyu.” Haka wasu abokan ta su ka rubuta, kuma jaridar Thisday ta wallafa.

Ta kuma bayyana dalilin da ya sa ta yi shiru ba ta ce komai ba sai yanzu.

Moyo ta ce duk karya ce ake yi mata domin a bata mata suna.

“Har yanzu yara biyu da sunan sa su ke amfani. Allah kadai ya san dalilin mutuwar Thomas. Kuma ba ni da masaniya ballantana na fadi, ko wani ya ce ga dalilin mutuwar Thomas, ba tare an gabatar da kwakwarar hujja ba.

“Duk da mun rabu, ba mu bari wani sabani ko rashin jituwa ya shiga tsakanin mu ba, ta yadda har zai shafi ‘‘ya’yan mu. Amma abin takaici sai aka bi mu da bi-ta-da-kulli, ana fallasa hotunan wadannan yara a soshiyal midiya.

“Ina yi wa iyalan sa ta’aziyyar rashin sa, da fatan za su jure rashin sa. Ina kuma rokon a bar mu haka nan mu ji da alhinin rashin sa.” Inji ta.

Tuni dai PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin an nada Shugabar Rikon Bankin FCMB, bayan sauke Adam Nuru, wanda aka zarga da haihuwar ‘ya’ya biyu da matar ma’aikacin bankin.

Bankin FCMB ya nada sabuwar Manajan Darakta, bayan tura shugaban bankin, Nuru Adam zuwa gida da aka yi, domin ya sauka a yi binciken zargin sa da ake yi da dirka wa matar ma’aikacin sa ciki sau biyu.

Wadda aka nada din dai mace ce mai suna Yemisi Edun, dadaddiyar ma’aikaciyar bankin ce.

Za ta ci gaba da rikewa ne har zuwa lokacin da aka kammala binciken Adam Nuru.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Bankin FCMB na binciken Shugaban bankin kan zargin ya haifi ’ya’ya biyu da matar wani ma’aikacin sa.

Wancan rahoton ya tabbatar ca cewa akalla mutum 1400 ne ya zuwa yanzu su ka sa hannu a kan takardar kiraye-kiraye ga Babban Bankin Najeriya, CBN cewa a kori Adam Nuru daga Shugabancin bankin FCMB.

Bukatar hakan ta taso ne bisa wani zargi da korafi da aka yi a rubuce cewa ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum mai suna Tunde Thomas.

An hakkake cewa Thomas ya mutu ne a ranar 16 Ga Disamba, sanadiyyar kududun bakin ciki da bugun zuciya, bayan da matar sa ta bayyana masa cewa, ’ya’ayan su guda biyu, ba na sa ba ne, domin ba cikin sa ba ne. Ta shaida masa kai-tsaye cewa ogan sa Adam Nuru, Shugaban Bankin FCMB na Najeriya, shi ne ya yi cikin yaron na farko. Sannan kuma shi ma dan na biyu, duk Nuru din ne ya dirka mata cikin ta haife su.

Cikin takardar korafin, an yi zargin cewa matar Thomas mai suna Moyo ta shaida masa cewa ga ta can ta kama hanyar zuwa Amurka tare da yaran su biyu.

An ce bayan ta isa Amurka, ta kira shi a waya tare da shaida masa cewa yaran nan fa biyu ba shi ne ya yi cikin su ba

Takardar korafin ta ci gaba da cewa bakin ciki ya sa Thomas ya samu cutar shanyewar rabin jiki, amma daga baya ya murmure, har ma ya fara neman auren wata mata.

“Tunde Thomas ya mutu makonni biyu bayan ya yi fama da matsananciyar damuwa.

“Saboda haka yaran nan biyu da matar sa Moyo ta haifa, ba na sa ba ne, ’ya’yan Adam Nuru ne, Shugaban bankin FCMB, shi ne farkan da ya rika neman ta, kuma ta haifi yaran biyu da shi.

“Tunde bai dade da zama darakta ba a FCMB. Makonni biyu da su ka gabata, ya koma gida daga wurin aiki, kawai sai ya yanke jiki ya fadi, ana sauran kwanaki biyu kacal a daura auren sa da budurwar sa, wadda a yanzu haka ta na dauke da cikin sa.

Takardar korafin ta yi zargin cewa Shugaban FCMB na ta kokarin binne maganar, domin kada abin ya fito fili har ya shafi aikin sa da mutuncin sa.

Tuni dai wani lauya mazaunin Akure, babban birnin Jihar Ondo mai suna Bolanle Cole, ya fara kamfen din neman babban Bankin Najeriya, CBN ya tsige Adam Nuru daga shugabancin ‘First Monument Commercial Bank’.

Ya yi barazanar bayar da makonni biyu a tsige Adam Nuru ko kuma ya fara kamfen din kaurace wa FCMB daga kwastomomin bankin.

PREMIUM TIMES ta tuntubi Kakakin FCMB Diran Olojo, wanda ya ce su na bibiyar salsalar wannan bahallatsa.

Share.

game da Author