Dakataccen Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya ki amsa gayyatar da Hukumar Ladaftar da Ma’aikata ta Kasa (CCB) ta yi masa.
CCB ta aika wa Magu wasikar neman ya bayyana a gaban ta, a ranar 17 Ga Nuwamba, a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
CCB ta zargin Magu da karya ka’idar aikin gwamnatin tarayyar Najeriya.
Gayyatar da CCB ta yi wa Magu na cikin wata wasika da aka tura masa, wadda daraktan binciken kwakwaf da sa-ido na hukumar ya sa wa hannu.
Hukumar ta nemi Magu ya kai mata takardun shaidar adalin kadarorin da EFCC ta karba a hannun wadanda su ka wawuri kudin gwamnati, su ka sayi kadarori da kudaden.
An kuma nemi ya je da dukkan takardun gidajen ko kadarorin baki daya.
CCB ta ce ta gayyaci Magu ne a karkashin doka ta 137, 138 (a), (b) ta Kundin Dokar Najeriya ta 1999.
Babban Lauyan Magu, Wahab Shittu, ya ce bai sani ba ko Magu zai amsa gayyatar ko ba zai amsa ba, domin bai sanar da shi wasikar gayyatar ta sa da aka yi ba.
Sai dai kuma yayin da PREMIUM TIMES ta dira hedikwatar CCB a ranar Talata da safe, domin ta dauko rahoton isar Magu ofishin, bai kai kan sa din ba.
Wasu majiyoyi a CCB da su ka nemi a sakaya sunayen su, saboda ba a ba su iznin yin magana da dan jarida ba, sun ce Magu bai aiko wasikar bayar da uzirin ki ko kasa halartar da ya yi ba.
“Ba mu samu wasikar neman uzirin kin halarta daga Magu ba, domin tun safe mu ke ta zaman sauraren isowar sa.” Haka wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES a ranar Litinin.
PREMIUM TIMES ta kasa samun kakakin yada labarai na CCB, Adetola Olusegun da kuma Magu shi kan sa.
A ranar Litinin PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa ranar Juma’a mai zuwa Kwamitin Binciken Magu wanda Tsohin Babban Alkalin Kotun Daukaka Kasa Ayo Salami ya jagoranta, zai mika wa Shugaba Muhammadu Buhari sakamakon binciken sa.
Discussion about this post