Kotu ta yanke wa barawon doyan da ya kashe mai gona hukuncin kisa

0

Babbar kotun dake Ado Ekiti jihar Ekiti ta yanke wa wani matashi dan shekara 26 mai suns Dele Ojo hukuncin kisa ta hanyar rataya a dalilin aikata kisan kai da yayi.

Alkalin kotun Abiodun Adesodun shaida cewa ya yanke wannan hukunci ne bisa ga hujjojin da aka gabatar a gaban sa a kotun da suka tabbatar da cewa tabbas Dele ya aikata wannan aika-aika ranar 13 ga watan Satumbar 2018.

Mai gonar doyan da Dele ya je sata gonarsa ya dade yana fakon barawon da ke hake masa doya domin kusan kullum idan ya garzaya gonar sai ya isake an yi masa barna.

Ranar ko da dubun Dele ya cika sai caf aka kamashi yana hakar doyan yana dankara wa a wani shirgegen buhu.

Daga nan sai mai gona, Adebowale da yake ya gane Dele ne ya ke masa sata, sai ya kwala masa kira yace Dele, Dele, juyawan Dele ke da wuya sai ya dirka masa wata bindigan da yake rike da ita ya arce abinsa.

Adewole ya rasu a asibitin Ijero dake Ekiti.

Lauyan da ya shigar da Karar, Wale Fapohunda ya gabatar da wasu kwararan hujjoji da a ciki akwai bayanan likita da na ‘yan sandan da ya nuna shi Dele ne barawon doyan kuma shine ya kashe Adewole.

Share.

game da Author