Kotun Ingila ta daure mai Kamfanin mai na ‘Rahamaniyya Oil’

0

Kotun Ingila ta yanke wa Abdulrahman Bashir, Shugaban Rahamaniyya Oil daurin watanni 10 a gidan kurkuku.

Cikin watan Fabrairu ne Mai Shari’a Butcher na Babbar Kotun Ingila da Wales ya yanke hukuncin dauri a kan mai Rahamaniyya saboda kotu ta same shi da laifin raina kotu da karya umarnin kotu ba sau daya ba ya yi, a wata shari’a da kamfanin mai na Sahara Energy Resources Ltd su ka maka kara a kotun.

“Makasudin wannan hukuncin daurin da aka yi wa Abdulrahman Bashir, saboda:

1. Ya bijire wa umarnin Mai Shari’a Robin Knowles ya bayar a kan sa a ranar 1 Ga Agusta, 2019.

2. Ya kangare wa umarnin da Mai Shari’a Bryan ya bayar a kan sa, a ranar 6 Ga Satumba,2019.” Haka alkalin da ya yanke masa wannan hukuncin daurin ya bayyana.

Me kotu ta ce ya yi amma ya ki yi, har ta daure shi?

Kotu ta bada umarnin cewa mai Rahamaniyya Oil and Gas bai wa kamfanin Sahara Energy Resources Ltd metrik tan 6,400.69 na man gas.

Kotu ta nemi Abdulrahman Bashir ya sa kamfanin sa Rahamaniyya Oil and Gas ya bada wannan lodin dimbin mai a tashar lodin jirage masu jigilar mai ta bakin ruwan Kirikiri, Apapa da ke Lagos.

Bashir ya karya wannan umarni ta hanyar kasa bai wa kamfanin sa Rahamaniyya Oil and Gas umarnin bada man gas din ga Sahara Energy, a tashar jiragen ruwa ta Apapa.

Yanzu haka PREMIUM TIMES HAUSA ta mallaki kwafe-kwafen takardun shari’a da hukuncin daurin da aka yi wa mai Rahamaniyya.

Har ila yau, cikin hukuncin da kotun ta yanke, Mai Shari’a ya ce za a iya sassauta masa zaman kurkuku zuwa watanni shida, idan ya bi umarnin da kotu ta gindaya masa, har ya bada adadin man gas din da kotu ta ce ya bai wa Sahara Energy.

Rahamaniyya: Ga Dauri Ga Kuma Tarar €500,000: Shi kuma Adebowale Aderemi, wanda shi ne Manajan Rahamaniyya, an ci shi tarar €10,000.

Asalin Rikicin Da Yadda Ya Tirnike:

CIkin watan Yuli, 2019 Ultimate Oil and Gas, wanda reshe ne na Rahamaniyya, ya kulla yarjejeniya a rubuce shi da Sahara Energy. A cikin yarjejeniyar an rattaba cewa kamfanin Rahamaniya zai rika adana wa adana man gas a rumbun ajiyar ta da ke tashar jiragen ruwa ta Lagos, har sai bayan Ultimate ya gama biyan kudaden.

Bayanan kotu sun nuna cewa a bisa yarjejeniyar da aka kulla, Sahara Energy ya tura metrik tan na man gas har 14, 967, 159 ga Rahamaniyya a tashar jiragen ruwa, a Lagos.

Sahara Energy ya aika da rasidin shaidar ya aika da man gas a ranar 26 Ga Disamba, 2019, kuma ya nemi a biya shi kudin sa har dala milyan 10,760,768 77.

Ranar 29 Ga Agusta, 2019 ne ya kamata a ce an biya kudaden gaba daya

Takardun kotu sun nuna yadda aka rika kai-ruwa-rana wajen biyan kudade.

PREMIUM TIMES ta gano cewa tun ma daga nan Najeriya ne aka fara shigar da karar laifin karya ka’idojin da ke shimfide a cikin jarjejeniyar da suka kulla.

Yayin da aka ci gaba da shari’a a Babbar Kotun Ingila, sai Bashir mai Rahamaniyya ki bin unarnin kotu ba sau daya ba, ciki har da hukuncin da ya daure shi a kurkuku.

Maimakon Rahamaniyya ya bi doka, sai ya nemi kotu ta janye hukuncin da ta yanke a kan ta a bisa abin da ya kira uzirin rashin lafiya da rashin isar da sako kan lokaci.

Daga nan mai Rahamaniyya ya yi alkawarin biyan kudin. Daga baya kuma ya sake yin watsi da batun kudaden.

An yi ta tsugune-tashi da lauyan Rahamaniyya a kotu, shi kuma ya ki gabatar da kan sa, ballantana ya biya kudaden.

Bayanin Lauyan Rahamaniyya ns Ingila:

Uzurin Da Lauyan Rahamaniyya, Andrew Thomas Ya Bayar:

“Ya kasance abu mai matukar wahala kafin Rahamaniyya ya samu lauya a Ingila, wanda ko da ya samu din, sai ya dauki tsawon lokacin da zai yi nazarin shari’ar sannan ya san matsayar da zai dauka.

“A lokacin da ya samu lauya a Ofishin Simon Berhel, an samu cikas din yadda za a iya turo masa kudi daga Najeriya zuwa nan Ingila domin ya samu somin-tabin da zai fara aiki.” Inji Thomas, cikin bayanin da ya yi wa kotu.

“Sannan kuma haramta zirga-zirgar sufuri a duniya da aka yi, tsawon lokaci saboda cutar Coronavirus ya haifar da tsaikon shirye-shiryen aikin lauyan Rahamaniyya gaba daya.” Inji Thomas.

Ya kara da cewa mai Rahamaniyya ya kasa bude e-mail din sa, saboda gyare-gyare da ake yi a kamfanin sa. Sai kuma shawarar da likitan sa ya ba shi cewa ya kwanta a gado ya huta tsawon watanni hudu, saboda matsalar rashin lafiyar sa.

Bayan Mai Shari’a Jacobs ya gama sauraren bayanan lauyan Rahamaniyya, ya ki amincewa da kuma gamsuwa da shi, ta hanyar bada misalai cewa lauyan Sahara Energy ya gabatar da hujjojin cewa dukkan sakonnin da aka aika masa ta e-mail ya same su.

Sannan kuma ya ce bai gamsu da cewa akwai wata wahala ko daukar tsawon lokacin da mutum zai yi kafin ya samu lauya a Ingila ba.

Haka nan batun rashin lafiya a matsayin hujja, ba ta gamsar da alkali cewa ita ce ta haddasa shi raina umarnin kotu, kin bin umarnin kotu da kuma kin biyan kudaden da ake bin kamfanin Rahamaniya ba.

“Haka nan ni ban gamsu cewa uzirin rashin lafiya ce ya hana Bashir Rahamaniyya kin zuwa sauraren karar da kuma bijire wa zuwa kotu a sauran lokutan zaman kotun, har zuwa ranar da aka yanke masa hukuncin dauri.

“Saboda haka na yi fatali da dukkan uzirin da wanda ake kara ya bayar ba.” Inji Mai Shari’a.

PREMIUM TIMES HAUSA ba ta tabbatar ko Rahamaniyya ya mika kan sa ga mahukuntan Ingila ba, ko kuma ya yi layar zana.

Share.

game da Author