Shugaban kasar Amurka ya Donald Trump yayi kira ga likitocin kasar da su rika ba mutanen da suka kamu maganin zazzabi da aka sani mai suna Chloroquine domin warkar da coronavirus.
Trump ya ce wannan an yi amfani da maganin a kasar Chana, kuma ma dai idan har bai yi aiki ba ba zai kashe mutane ba.
Saidai kuma hukumar kiwon Lafiya ta Duniya WHO ta ce ba a gama bincike akai wannan magani ba da tabbatar da ko yana maganin coronavirus.
A kwai akalla mutane 9000 da suka kamu da cutar a kasar Amurka, kuma mutum sama da 150 sun mutu.
A ranar Alhamis Jami’ar John Hopkins dake kasar Amurka ta bayyana cewa mutane sama da 200,000 ne ke dauke da cutar coronavirus a fadin duniya.
A dalilin haka kasashen duniya da dama sun hana jiragen sama sauka da tashi a kasashen su, sun rufe iyakokin kasashen su na kasa sannan wasu sun kafa dokar hana walwala domin dakile yaduwar cutar.
Bisa ga rahoton, mutane 201,000 ne suka kamu da cutar sannan 8,000 sun mutu.
Rahoton ya kuma bayyana cewa kasar Chana da a nan ne cutar ta fara barkewa ta fara samun ragowar yaduwar cutar.
Duk da haka kasar ce ta fi kowacce kasa a duniya yawan mutanen da suka kamu da cutar da yawan wadanda suka mutu.
Zuwa yanzu mutane 82 suka warke daga cutar sannan 3,000 sun mutu.
Italiya ce kasar dake biye da Chana inda a kasar mutane 31,500 suka kamu da cutar, 2,500 sun mutu.
Ma’aikatan kiwon lafiya sun yi kira ga kasashen duniya da su karfafa matakan hana yaduwar cutar amma kuma wasu kasashen duniya na kukan rashin isassun kayan gwajin cutar.
Idan ba a mata a ranar Laraba ne ba kungiyar kiwon lafiya (WHO) ta sanar cewa mutane 600 ne ke dauke da cutar sanna 41 sun warke a kasashen Afrika.
WHO ta kuma sanar ranar Alhamis cewa a cikin awa 24 mutane 17 sun mutu sannan mutane 633 na dauke da cutar a Nahiyar Afrika.
Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.
Za a iya kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.
A rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.