An kara kama ‘yan Kungiyar Ansaru 3 da ake zargin kai wa Sarkin Potiskum hari

0

Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa ta bayyana kama wasu ‘yan ta’addar ‘Ansaru su uku da ta ke zargi su na da hannu dumu-dumu wajen kai harin yunkurin yin garkuwa da Mai Potiskum, Umar Bubaram.

Kakakin ‘Yan Sanda na Kasa, Frank Mba, ya bayyana haka a ranar Lahadi cewa an damke Munkailu Liman Isah, mai shekaru 31, Abdullahi Saminu da aka fi sani da Danmunafiki mai shekaru 21 da kuma Aminu Usman shi ma mai shekaru 21.

Ya ce am kama su sakamakon wasu bayanai na sirri bayan da ‘yan sanda suka yi wa ‘yan kungiyar Ansaru kakkabar-‘ya’yan-kadanya a Dajin Kurudu da ke Birnin Gwari, Jihar Kaduma.

Ya zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sanda ta ce ta na tsare da mutane 8 kenan masu hannu a harin da aka kai wa Sarkin Pataskum da dare, a kan hanyar sa ta zuwa Zaria daga Kaduna, cikin watan Janairu.

Mba ya nuna takaicin yadda suka gano wasu jama’a na huldar hada-hadar cinikayya da ‘yan Ansaru.

“Abin bakin ciki har kayan sayarwa ake kai musu har a can cikin mafakar su.” Inji Mba.

Ya ce jami’an tsaro na nan na ci gaba da bincike, kuma za a gano dukkan masu hannu a wannan hari.

PREMIUM TIMES tun a lokacin dai ta buga labarin yadda aka yi yunkurin yin garkuwa da Sarkin Potiskum, amma ba a yi nasara ba.

An kashe mutane hudu a cikin tawagar sa. Kuma a lokacin wannan harin ne aka kididdige cewa an yi kashe mutane da suka hada da matafiya har 30 tare da yin garkuwa da mutum 100 a hare-haren da aka addabi jama’ar yankin da su a wancan dan lokaci.

Share.

game da Author