CIKIN 2019: Yadda ICPC ta kwato naira biliyan 77 daga hannun barayin gwamnati

0

Hukumar Zakulo Masu Wawurar Kudaden Gwamnati (ICPC), ta bayyana cewa a cikin shekarar 2019 ta yi nasarar kwato naira biliyan 77 daga hannun barayin gwamnati.

Sai dai akasarin wannan adadi ba ruwan madarar kudaden ba ne, “kadarori ne da aka kwace daga wurin wadanda suka wawuri kudaden.” Injin ICPC.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata taswirar yadda aka kwato kudaden dalla-dalla (Infographic), wanda ICPC din ta aiko wa PREMIUM TIMES.

“An samu nasarar kwato adadin kudaden daga wasu samame da mu ka kai kan wasu da suka wawuri kudaden jama’a da kuma kadarorin wadanda kotu ta bada umarni aka kwace, bayan ta tabbatar da cewa kudin da aka sayi kadara da su, na gwamnati ne.

” ICPC na kuma yi nasarar hana ma’aikatu da hukumomin gwamnati da cibiyoyi sama da 200 yin almubazzaranci da kusan naira bilyan 41.98.”

Kakakin Yada Labarai ta ICPC, Rashidat Okoduwa ta yi wa PREMIUM TIMES karin haske cewa hukumar ta kuma cika da mamakin yadda wasu ma’aikatu da hukumomi suka kafci kudaden da suka rage ba su kashe ba a karshen shekara, su ka gabza wa ma’aikatan su a matsayin bashi, ba tare da umarnin gwamnati ba.

“Da muka bankado wannan, sai muka sanar da Ma’aikatar Harkokin Kudade cewa ta hana wadannan hukumomi da ma’aikatu sake kai hannun su a kan ko da naira dubu daya daga cikin kudaden.”

ICPC ta ce ta kwato naira bilyan 1. 2, sauran kuwa duk kadarori ne, da suka hada da maka-makan filaye, kantama-kantaman gidaje da kuma tsala-tsalan motocin alfarma da aka saya da kudaden sata daga aljihun gwamnati.

“Mun samu korafe-korafen 1934 cikin shekarar 2019. Mun binciki 580, kuma mun gurfanar da mutum 83 a kotu.” Inji ICPC.

Share.

game da Author