Babbar Kwamandar Makarantar Sakandaren Sojojin Sama da ke Jaji Kaduna, ta bace.
Wata sahihiyar majiya a cikin hukumar tsaro ta sojoji ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Naval Commodore O.O Ogunlana ta bace kwanaki da dama, kafin a Ankara da bacewar ta a ranar Litinin da ta gabata.
Majiyar ta tabbatar da cewa Mrs. Ogunlana, wadda matar aure ce, ita ce mai lambar Sojojin Ruwan Najeriya NN/2367. An daina gani ta ko jin duriyar ta tun daga ranar 13 Ga Satumba.
An kara shiga zullumin bacewa ko rashin ganin ta ranar Litinin, yayin da ba a gan ta a ofishin ta ranar Litinin din ba.
Har ila yau, majiyar kara da cewa ba a tabbatar da bacewar ta ba, har sai da aka je gidan ta da ke Lamba 22, AVM Also Crescent, sannan aka kara tabbatar da cewa ba a san inda ta ke ba.
“Rabon da a sa ta a ido tun ranar Juma’a, 13 Ga Satumba, a cikin harabar makarantar wadda ke cikin bariki.” Inji majiyar Premium Times.
“An kai rahoton rashin ganin ta, bayan an yi ta buga lambar wayar ta. Wayar ta na kara, amma ba ta dauka ballantana ta amsa kiran.”
An bankara kofar gidan na ta da karfin tsiya, yayin da aka ji wayar ta na kara daga cikin gidan ta.
Sai dai kuma majiya ta ce ta na da wasu lambobi biyu, na Glo da Airtel, wadanda aka yi ta kokarin kira, amma ba a samun ta.
Sannan kuma an duba ba a ga motar ta, kirar Toyota Highlander ba, mai lambar Legas, AAA 434 CF.
Premium Times ta gano cewa hukumar kwalejin na ta korarin gano inda duk ake tunanin ta ke.
Sannan kuma wasu a cikin barikin na nuna matukar damuwar da tunanin cewa ko garkuwa da ita aka yi.
Sai dai kuma Hedikwatar Sojojin Ruwa ta Kasa ta nuna kamar ba ta san abin da ake ciki ba, domin Kakakin Sojojin Ruwa, Suleiman Dahun ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa har zuwa lokacin da aka tambaye shi, labarin bacewar babbar jami’ar sojan ruwan bai je masa ba.
“Maganar gaskiya ban san komai dangane da wannan labari ba. Za ka iya kiran Jami’in Yada Labarai na Jaji domin jin karin bayani.” Inji Dahun.
Duk wani kokarin jin ta bakin Jami’in Yada Labarai na Jaji, Kaduna bai yiwu ba har zuwa lokacin da aka rubuta kuma ka buga wannan labari.