A sakamakon bincike da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi ya nuna cewa sakacin da ma’aikatan kiwon lafiya kan yi a lokacin da suke duba marasa lafiya a asibitoci na cutar da wadannan marasa lafiya akalla mutum hudu cikin 10.
Wannan matsala ya dade yana ci wa WHO tuwo a kwarya ganin cewa hakan kan yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama saboda skaci da ganganci.
A dalilin haka kungiyar ta tsayar da ranar 17 ga watan Satumba a matsayin ranar wayar da kan mutane da ma’aikatan kiwon lafiya sanin muhimmanci ba mara lafiya kulana musamman a asibitoci.
Shugaban WHO Tedros Gherberyesus ya fadi cewa matsalolin da suka hada da rashin daukar kwararrun ma’aikata, rashin horas da ma’aikata, rashin mai da hankali wajen yi wa mutane gwaji da dai sauransu na daga ciki abubuwan da ake fama da su a asibitocin kasarnan.
Sannan ya kara da cewa a dalilin haka akan samu wasu likitocin da ke ba marasa lafiya maganin da ba na abin da ke damun su bane. Daga karshe sai kaga an fada cikion mummunar matsala na rashin lafiya ko kuma ma mutum ya rasa ransa.
Gherberyesus yace bincike ya nuna cewa a kalla mutane biyar ne kan rasa rayukan su a asibitoci a dalilin sakacin ma’aikatan kiwon lafiya.
Yadda ma’aikatan kiwon lafiya da likitoci ke nuna halin ko in kula ga marasa lafiya a asibitocin kasar nan baya misaltuwa. Da yawa daga cikin masu hali kan gwamnace su fita zuwa kasashen waje domin ziyartar asibiti idan basu da lafiya duk saboda babu asibitoci da ma’aikata nagari a kasar.
Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa gwamnati ba za ta yi kasa-kasa ba wajen ganin ta inganta fannin kiwon lafiyar kasarnan.