TITIN LEGAS ZUWA IBADAN: Har yau kashi 40 bisa 100 aka kammala -Gwamnati

0

Babban Jami’in Lura da Titinan Gwamnatin Tarayya a Legas, Ademola Kuti, ya bayyana cewa har zuwa an cimma nasarar kammala kashi 40 bisa 100 kadai na aikin gyaran titin Legas zuwa Ibadan.

Titin Legas zuwa Ibadan dai a da nisan sa bai wuce kilomita 129 ba. An fara aikin sa tun cikin 2013 a bisa yarjejeniyar kammala shi cikin 2017. Yanzu kuma an ce ko a iya kammala shi sai cikin 2021 ko 2022.

Kuti ya ce a baya an sha fama da matsalar kudade da kuma neman inda za a samu kudin aikin.

“To abin da ya kara kawo tsaikon rashin kammalawa da wuri, saboda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta shigo da karin wasu ayyuka a cikin aikin hanyar. Akwai karin gadoji da kuma gadojin sama. Sannan akwai shingen karbar kudaden haraji a hannun direbobi da kuma karin fadada hanya.”

Kuti ya ce ita kanta hanyar Ikorodu zuwa Shagamu da ake so direbobi su rika bi, idan an rufe wani yanki na titin Legas zuwa Ibadan a yau Litinin, kashi 18 bisa 100 aka kammala.

Sai dai kuma ya ce an saisaita inda duk ake ganin za a iya samun cinkoso a hanya. Kuma ya yi kira ga direbobi su rika bin ka’ida tare da bada hadin kai ga ‘yan kwangila masu aikin titi.

Jama’a da dama na nuna damuwa a kan rashin gaggauta aikin titin Abuja zuwa Kano, mai tsawon kilomita 400.

Su na ganin idan har Gwamnatin Buhari za ta kintaci shekarar 2022 za ta iya kammala aikin titin Legas zuwa Ibadan mai tsawon kilomita 129, to sai nan da shekara nawa za a kammala titin Abuja zuwa Kano kenan.

Cinkoson motoci

Kuti ya ci gaba da cewa cinkoson motoci a Legas ya fi na sauran garuruwan kasar nan muni da kashi 70 bisa 100.

Ya ce wannan cinkoson motoci na masu shiga da fita da Legas da na cikin garin Legas duk na daga cikin babban dalilin samun matsaloli a aikin gyaran titina a Legas.

Ya ce ita kanta Jihar Legas karama ce, sai yawan al’umma. Sannan kuma akwai wahala sosai wajen kokarin aikin shawo kan inda motoci suka cinkushe.

Share.

game da Author