BAYAN WATA DAYA: Har yau ba a san inda aka gudu da mai sukar Ganduje ba

0

Sama da wata daya bayan da wasu dauke da bindigogi suka gudu da Abubakar Idris, har yau babu amo, babu labarin inda aka arce da shi.

Abubakar, wanda aka fi sani da Dadiyata, malamin jami’a ne, mazaunin Kano. Ya yi suna sosai wajen caccakar Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da salon mulkin sa.

Ya na a sahun gaban masoya Rabiu Kwankwaso, kuma dan Kwankwasiya ne da ke gode wa Kwankwaso saboda daukar nauyin karatun sa da ya yi.

Wajen karfe 1:00 na dare wasu dauke da bindiga suka je har gidan sa cikin shigar-burtu suka sace shi, a cikin motar sa, suka gudu.

Da farko an rika yada ji-ta-ji-tar cewa jami’an SSS ne suka tafi da shi. Sai dai kuma a yanzu matar sa ta ce ta na cikin da damuwa ita da yaran ta biyu.

“A kullum addu’a mu ke yi Allah ya fito da shi. ‘Yan sanda kuma kullum ce mana suke yi suna baking kokarin su.

” Ya’yan sa kullum kukan son ganin baban su su ke yi”. Inji ta.

Kakakin Yada Labarai na ‘Yan sandan Kaduna, Abubakar Sabo, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa, “to wannan lamari dai ba irin garkuwar da kowa ya sani ana yi ba ce. Domin har yau babu wadanda suka fito su ka ce ga abin da za a biya su. Kuma ba su ce ga halin da Abubakar ke cikiba.”

Abubakar ya kasance ya na sa-in-sa da magoya bayan Ganduje sosai a soshiyal midiya. Sace shi da aka yi ta sa guyawun jama’a da dama sun yi sanyi.

Ita ma jam’iyyar PDP ta yi kira da a gaggauta nemi Abubakar Dadiyata, a duk inda ya ke.

Share.

game da Author