Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Assalamu Alaikum
Ya ku jama’ah! Mun samu labari daga majiya mai tushe, kuma mai karfi cewa, Gwamnan Jihar Kano yana neman yanke duk wata hulda tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da ta Jihar Rivers.
Gwamnatin Ganduje na shirin yanke duk wata hulda ta cinikayya ko kwangila da sauran al’amurra tsakanin ta da gwamnatin Jihar Rivers. Majiyar mu ta shaida muna haka ne bayan wata ganawa da wani babban makusancin Gwamna Ganduje wanda ya tabbatar muna da yadda wai Gwamnan ya nuna damuwar sa sakamakon rushe wancan Masallacin da Al’ummar Musulmi suke Sallah.
Magoya bayan Gwamna Ganduje suna nan suna ta yada farfaganda domin jawo wa gwanin na su farin jini a wurin al’ummah, ganin irin bakin jinin da yake da shi, sakamakon wasu matakai da yake dauka da ba su yiwa mutane dadi ba; wai suna cewa Gwamnan ya nuna bacin ransa bayan rushe wancan Masallaci, inda ta kai wai har ya dauki waya yayi magana da Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike akan ya mayar da ginin wancan Masallaci, amma Gwamna Wike yayi biris da shi!

Wanda daga karshe magoya bayan Gwamna Gandujen suke cewa wai, yayi taron manema labarai ya nuna bacin ransa. A yammacin wannan rana Ganduje yayi taro da Jami’an gwamnatin sa, a inda ya bukaci su tsayar da duk wata harkalla da wata hulda dake tafiya tsakanin Jihar Kano da ta Rivers.
Suka ce wai kawo yanzu shirye-shirye sunyi nisa, tuni Ganduje yayi cinikin wani katafaren gida a Jihar Rivers domin mallakawa Musulmin Jihar, a madadin wancan Masallacin kafin daukar matakin Shari’a akan Gwamnan Jihar Rivers.
Wannan al’amari dai jama’ah da dama suna kallon siyasa ce kawai yasa Gwamna Ganduje daukar wadannan matakai. Domin Gwamnan yana sane da bakin jinin da yake da shi, da kaurin sunan da yayi a wurin al’ummah, sanadiyyar harkallar zargin sa ake yi da karbar cin hanci na miliyoyin daloli, da kuma matakin da ya dauka na fada da masarautar Kano mai dimbin tarihi da daraja a Jihar Kano da ma arewacin Najeriya baki daya, karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.
To duk dai mutane suna fassara wannan daukar mataki da Gwamnatin Jihar Kano ta yi domin kokarin wanke wadancan laifukan da suka jawo mata bakin jini a wurin al’ummah. Wanda tattaunawar da muka yi da jama’ah, ra’ayin mutane ya nuna cewa, wancan laifi na Ganduje da wahala ya wanku, domin wannan fada da yake yi da Gwamna Wike, siyasa ce kawai, ba domin Allah yake yi ba. Har suna cewa Gwamnan na Kano yana so kawai ne ya yaudari mutane ne da sunan addini.
To ya ku jama’ah, duk dai yadda ta kaya, zamu kawo maku In Allah yaso.
Nagode,
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya.
Za’a iya samun sa a adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.
Discussion about this post