Cikin minti hudu mu ke sace kundun kwakwalwar kowace mota –Wasu barayi

0

Zaratan ‘yan sandan RRS a Jihar Legas sun yi nasarar damke wasu rikakkun barayi biyu da suka kware wajen iya kwance kundun kwakwalwar mota, wato ‘brain box’ a cikin mintina hudu kacal.

An damke Sodiq Musa dan shakara 28 da kuma Saidu Atiku mai shekaru 34, dauke da kundun akwatan kwakwalwar mota (brain boxes) guda uku.

Na cikon ukun su mai suna Ridwan Adamu ya tsere dauke da kunun ‘brain box’ guda daya a hannun sa. hakan ya nuna kenan an same su da ‘brain boxes’ guda hudu kenan.

An kama su a kan Titin Awolowo, Ikeja, Lagos a gida mai lamba 27. Dukkan ‘brain boxes’ din dai na motocin Tayota ne.

Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Musa, ya yi ikirarin cewa ya kammala karatun digirin farko a jami’a, amma cikin 2017 ya nausa zuwa Legas domin neman kudi.

“Da wani irin dutse ne mu ke amfani. Sai mun fara raba wutar fulogi tukunna, don kada a ji karar motar. Minti biyu kacal ya ishe mu kwance ‘brain box’ na Toyota Hiace. Idan Toyota Hilux ce kuwa ba mu wuce minti hudu.”

Haka Musa ya bayyana wanda Ridwan kafin ya shigar da shi hanyar sata, ya taba aikin gasa nama a wani otal

Ya ci gaba da shaida wa jami’an RRS cewa a baya can Atiku mai gadi ne a wani kamfani da ke kan titin da aka kamo su. Shi ne ya kira shi domin su sace ‘brain boxes’ na wasu motocin kamfanin.

Sun shaida wa jami’an tsaro cewa ‘brain box na Hilux ya na da tsada, domin ya na kai har naira 40,000.

“Masu son saye a wurin mu ba su yarda su shigo cikin kasuwa, sai dai mu ke zuwa mu same su a wajen kasuwa, mu sayar musu, su ba mu kudin mu, kowa ya kama gaban sa.

“Duk cinikin fa a cikin minti biyu ake yi a gama, su biya, mu ba su kowa ya bace kawai. Babu bata lokaci, saboda da su masu sayen a wajen mu da mu da ke satowa mu na saida musu, duk mun yarda a kan farashin da ake saye mu ke sayarwa.”

“Ridwan ke ba ni kashi 40 bisa 100 na kudin da aka samu. Sannan mun fi zuwa yi satar ‘brain boxes’ a wuraren holewa can wajen karfe 1:00 zuwa 2:00 na talatainin dare. A lokacin yawancin masu motocin duk sun yi mankas da giya a cikin wuraren holewar su.’

Za a gurfanar da su kotu da an kammala bincike.

Share.

game da Author