AMBALIYA: Ruwa ya kori dubban mutane daga gidajen su a Adamawa – ADSEMA

0

Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa (ADSEMA), ta bayyana cewa ruwan da aka sheka ranar Juma’ar da gabata, ya yi sanadiyyar asarar ga dubban jama’a da suka rasa muhallin su da dukiyoyin su.

Babban Sakataren ADSEMA, Muhammad Sulaiman ne ya bayyana wa manema labarai haka jiya Lahadi a Yola, babban birnin Jihr Adamawa.

Sulaiman ya ce har yanzu hukumar su ta na ta kokarin tantance yawan barnar da ruwan ya yi, da kuma dimbin jama’ar da ta fi shafa.

“ ASDEMA ta tattara wasu da suka rasa wurin kwanciya su 219 daga Modire da Yolde-Pate, wasu unguwannin marasa galishu da ke cikin Karamar Hukumar Yola ta Kudu.”

“ Sannan kuma har yanzu jami’an mu na kokarin tantance irin yawan ta’adin da ambaliyar ta yi a Kananan Hukumomin Yola ta Arewa, Girei, Ganye da Shelleng.” Inji Sulaiman.

Duk da ya ce har yau dai ba a samu rahotannin salwantar rayuka ba, amma ruwan ya barnata kayayyaki, gidaje, gonaki da amfanin gona da kuma dabbobi masu yawa.

A wasu kananan hukumomin ma kamar yadda Sulaiman ya bayyana, ruwan ya lalata hanyoyi da makarantun gwamnati.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kungiyoyin bada jinkai daban-daban su fito kawo agaji, domin kauce wa barkewar cututtaka a yankunan da ruwan ya yi barna.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya ruwaito yadda a farkon watan Agusta aka rayukan mutane shida a Yola, sakamakon ambayliyar ruwa.

A farkon wannnan wata kuma PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin gargadin da wasu hukumomi suka yi cewa akwai yiwuwar barkewar ambaliya cikin watan Satumba, a wasu jihohi 30, ciki har da Abuja.

Share.

game da Author