Hukumar Kwastan ta Kasa ta bayyana cewa kayan yakin da jami’an tsaron Najeriya suka damke a Adamawa, an yi niyyar shiga da su Jamhuriyar Nijar ne.
Kakakin Yada Labarai na Hukumar Kwastan, Joseph Attah ne ya yi wannan karin hasken, tare da cewa an damke dukkan direbobi shida da aka samu su a tuka motocin yakin.
An dai kama motocin yakin ne guda shida wadanda duk karfin nakiya ba ta iya tarwatsa su ko lahanta su, kuma aka damka su ga jami’an kwastan a ranar Asabar.
Kayan yakin an yi niyyar nausawa da su cikin Jamhuriyar Nijar ba tare da sanar da hukuma ba.
Ba a bayyana wa hukuma a rubuce wanda ke da kayan yakin ba, ko inda za a kai su, kafin sojoji su damke su a Karamar Hukumar Fufore, Jihar Adamawa.
Bayan an kama kayan yakin, sai sojojin Birged na 23 da ke Kolkol suka damka su ga jami’an kwastan.
Dama dai PREMIUM TIMES ce ta fara fallasa labarin yadda sojoji suka damke kayan yakin, bayan an damka wa jami’an kwastan su domin bincike.
Majiyar sojoji ta ce akwai shakku da tababar irin yadda aka yi kumbiya-kumbiyar fitar da kayan yakin ta tsakiyar yankin da ya shafe shekaru goma ya na fama da kashe-kashen Boko Haram.
Idan ba a manta ba, an samu tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibekunle Amosun da mallakar tulin bindigogi da dubban albarusai kafin ya sauka daga mulki.
Ya damka su ga ‘yan sanda ne kwana daya kafin ya sauka daga mulki, cikin watan Mayu, 2019.
Direbobin da ke jan motocin yakin sun shaida cewa sun bar Kamaru ne su na kan hanyar zuwa Jamhuriyar Nijar, domin kai wadannan motoci a can kasar.
“Da alama sun maida Najeriya bututun safarar makamai. To idan ma safarar za su yi, ai tilas sai an sanar da hukumomin da abin ya wajaba su sani a Najeriya, kafin ma a shigo da su a bakin iyakokin kasar nan.”
Sojoji dai sun ce har yau jami’an SSS ba su fitar da wani jawabi ba dangane da damke motocin yakin guda shida.