Gwamnatin Buhari ta fito da sabon lasisin daura aure

0

Gwamnatin Tarayya ta shigo da sabon Lasisin Daura Aure wanda ya kunshi dukkan nau’ukan aurarrakin da ake daurawa a Najeriya.

Babban Sakatare na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Georgina Ehuriah ce ya yi wannan sanarwa jiya, a lokacin da ta ke jawabi a wurin taron matakai da ka’idojin daura aure a Najeriya, a yau Laraba a Abuja.

Ta ce ma’auratan da ba su mallaki katin shaidar auren su ba, to za su iya bude shafin intanet na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, domin su sabunta lasisin na su.

Ehuriah ta kara da cewa ba dukkan wuraren ibadu ba ne aka amince su daina daura aure ba.

Daga nan sai ta shawarci ‘yan Najeriya su tabbatar da cewa sun daura aure wuraren da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta amince su rika daura aure.

“An shigo da wannan tsarin ne domin a maida daurin aure ya zama abu ne mai mai sahihiyar rajista a kwamfutar tattara bayanan kididdiga ta kasa.” Inji ta.

“Idan har ba babban jami’in kula da rajitar ma’aurata ne ya bayar da sakifiket ba, to duk wani satifiket haramtacce ne, kuma ba zai iya zama shaida a duk wuraren da mai su ke son yin amfani da shi.”

Daga nan sai ta kara da cewa wannan satifiket shi ne za a rika amfani da shi wajen neman iznin shiga wasu kasashe, idan matafiyi zai fiata daga Najeriya.

Ta ce duk wuraren ibadun da suka daura aure ba tare da izni ba, to sun karya dokar Najeriya.

Ta kuma kara da cewa masu kula da wuraren ibadu za a shawarce su da ku cika wasu sharudda tukunna, kafin a ba su iznin daura aure.

Sannan kuma ta yi korafin cewa ‘yan Najeriya ba su damu su rika yin rajistar auren su ba bayan sun yi auren addini ko na gargajiya.

Hakan inji ta na zame wa ma’aurata matsala a can gaba.

Share.

game da Author