Sakamakon binciken da wasu likitoci daga kasar Britaniya da Thailand suka yi a kwanakin baya ya nuna cewa zazzabin cizon Sauron da baya jin magani ya bullo a kasashen Asia da Afrika.
Sakamakon binciken ya nuna cewa magungunan ‘Artemisinin da Piperaquine’ da ake amfani da su wajenmaganin zazzabin basu aiki a jikin mutu.
Roberto Amato ma’aikacin ‘Wellcome Sanger Institute’ dake kasar Britaniya ya bayyana cewa cutar na yaduwa kamar wutan daji sannan yana da wahala a samu sauki idan aka kamu.
MATSAYIN NAJERIYA DA ZAZZABIN
Sakamakon bincike ya nuna cewa zazzabin cizon sauro ya yi ajalin yara ‘yan kasa da shekara biyar har 400,000 sannan da mata masu ciki sama da 1000 daya.
A yanzu haka zazzabin na ci gaba da yaduwa a Najeriya da wasu kasashen duniya 97.
Sakamakon bincike ya nuna cewa mutane miliyan 51 na dauke da zazzabin cizon sauro sannan akan rasa rayukan mutane 207,000 duk shekara a Najeriya a dalilin wannan cutar.
A yanzu dai Najeriya bata iya shawo kan matsalar ci gaba da yaduwar zazzabin ba koda akalla kashi 50 bisa 100 ne na cutar duk da dunbin kudade da ake warewa da tallafin da take samu daga kungiyoyindon dakile yaduwar cutar.
A kwanakin baya ne hukumar hana yaduwar zazzabin cizon sauro na kasa (NMEP) ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ware kudade domin ganin an kawar da zazzabin cizon sauro a kasar.
Jami’in hukumar Audu Mohammed ya sanar da haka a taro da aka yi a Abuja.
Mohammed ya ce rahotan cibiyar ‘World Malaria Report’ na shekarar 2017 zuwa 2018 ya nuna cewa an sami akasi game da aiyukkan kawar da cutar da kasashen duniya ke yi daga wadannan shekaru.
Rahotan ya nuna cewa a shekarar 2017 cutar ta yi ajalin mutane da yawa a kasashen Afrika da India.
Mohammed yace matsalolin da ake fadawa ne ya sa ya zama dole a ci gaba da kira ga gwamnati da ta maida hankali wajen ganin an dakile yaduwar cutar a kasar nan. a dalilin haka yake kira ga gwamnati da ta zage damtse wajen ganin an dakile yaduwar cutar a kasarnan.
Discussion about this post