TSARO: ‘Yan gudun hijira sun fara komawa garuruwan su a jihar Zamfara

0

A dalilin samar da zaman lafiya da jami’an tsaro suka yi ‘yan gudun hijira da dama sun fara komawa garuruwan su da suka baro jihar Zamfara.

Mataimakin gwamnan kan harkokin yada labarai Yusuf Idris ya sanar da haka a takarda da ya raba wa manema labarai ranar Juma’a.

‘Yan gudun hijiran sun koma kauyukansu dake Lilo, Fura Girke, Kowha, Kundumau, Yargeba da Bundugel tun a ranar Alhamis.

Babban maitaimakin gwamnan kan harkokin tsaro Alhaji Abubakar Muhammad Dauran ne ya jagoranci dawo da ‘yan gudun hijiran.

“ Da dama daga cikin ‘yan gudun hijiran sun yi zama a sansanonin dake garin Mada, karamar hukumar Gusau na tsawon watanni shida. Sannan wannan gwamnatin Matawalle ta tabbatar musu da tsaron rayukansu da dukiyoyin su.

Gwamnan jihar Bello Matawalle ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a dalilin karo jami’an tsaro da aka yi da kuma ci gaba da fatattakar mahara da dakarun Najeriya ke yi.

Matawalle ya kuma yi kira ga mutane kan ci gaba da yi wa jihar addu’a sannan ya yi kira ga manoma su fara shirin komawa gona domin zamn lafiya na dindindin ya fara dawowa jihar.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Gwamna Bello Matawalle ya gana da masana kuma kwararru a fannin tsaro a birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.

Cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Gwamna, mai suna Yusuf Idris ya yi ya ce gwamna ya tafi Saudiyya ya yi Umra, kuma daga nan zai yada zango a Dubai inda zai hadu da wasu kwararru a fannin magance tsaro domin su tattauna hanyoyin shawo kan matsalar.

“Gwamna zai gana da masana fannonin tsaro a Dubai domin neman shawarwarin hanyoyin da suka fi dacewa a kawo karshen wannan hare-hare, kashe kashe sa samamen garkuwa da mutane da suka addabi jihar Zamfara.

Share.

game da Author