Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi shi da Mataimakin sa Simon Achuba, sun ware wa kan su naira miliyan 14 a cikin kasafin kudin 2019, domin bukukuwan rufe gawarwaki.
PREMIUM TIMES ce ta binciko haka a cikin kasafin kudin jihar, wanda yanzu haka kwafen kasafin na Jihar Kogi na 2019 kakaf ya na hannun PREMIUM TIMES din.
Sai dai kuma ba a san ko gawarwakin su wa za a yi bikin biznewa da wadannan makudan kudade ba.
Daga cikin kudaden da aka ware za a kashe a ofishin gwamnan, an ware naira milyan 12 da aka ce za a kashe wajen bukukuwan rufe gawa.
Shi kuma ofishin mataimakin gwamna aka ware naira milyan 2, ita aka ce wajen bikin bizne gawa za a kashe su.
Wani abin daure kai kuma shi ne wata naira milyan 15 da aka sake warewa aka ce za a kashe su wajen “kama hayar gidaje.”
Akwai wasu zunzurutun naira milyan kuma a cikin kasafin kudin dai, wadanda a ka ce an ware su ne domin bayar da gudummawa, alhali kuma a wurare daban-daban an ware kudaden bayar da gudummawa ga kungiyoyi.
Misali, an ware wata naira milyan 70 domin bayar da tattafi ko gudummawa ga Kungiyar Tsoffin Sojoji; akwai ma wata naira milyan 10 da aka ware domin gudummawa ga masu bautar kasa (NYSC) dai wata naira milyan 10 ita ma da aka ce gudummawa ce ga marasa karfin iya ciyar da kan su da kuma naira milyan 50 domin bayarwa ga Gidajen Rainon Marayu.
Shi ma ofishin mataimakin gwamna an lasa masa naira milyan 2 domin raba wa marasa galihun iya ciyar da kan su, wata naira milyan 1 domin tallafi ga NYSC akwai kuma wata milyan daya domin gidajen rainon marayu.
Sai da Kakakin Yada Labarai na gwamnan mai suna Obogwu Mohammed, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba a yi kambamen-zulaken kudade wajen kasafin ba.
Ya ce sai da aka bi diddigi tirya-tiryan aka daddale, aka tabbatar an ware daidai adadin da suka dace, ba kamfata kawai aka yi ba.
Ya ce an ware miliyoyin kudaden bukukuwan rufe gawa ne domin bayarwa ga iyalan ma’aikatan cikin Gidan Gwamnati, idan kwanan wani ko na dan uwan wani daga cikin su ya kare.
Mohammed ya ce kudin ma da aka kebe domin bukukuwan bizne gawargwaki ai sun ma yi kadan, tunda na shekara daya ne cur, idan aka yi la’akari da yawan masu bukatar kudaden idan sun yi rashin wani daga cikin iyalan su.
Ya kuma bada misalin bizne gawar wani jami’in yada labarai a Gidan Gwamnati da ya rasu, kuma gwamnati ce ta dauki nauyin bizne shi.
Discussion about this post