Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya kwankwadi ruwan addu’o’i da fatan Alkhairi daga miliyoyin mutanen jihar Bauchi a ranar Asabar a dalilin fitowa da kan sa ana bude kwatoci da kwashe bola.
Matan aure da magidanta duk sun fito domin tsaftace gidajensu da titunan jihar.
Matasa ko sun fito kwansu da kwarkwatansu ne suka karade tituna suna bude hanyoyin ruwa da share-share tituna da kwararo-kwararo.
Shi kansa gwamnan jihar Bauchi da jami’an gwamnati ba a barsu a baya ba domin da kan su aka fito domin yin wannan aiki.
Gwamna Bala ko harda darewa katafila domin kwashe tarin bola a tsakiyar garin Bauchi.
Mutane da suka zanta da wakilin mubsun shaida mana cewa wannan irin shugabanci sun dade da dandana shi.
” Wannan salo na gwamnatin Bala a Bauchi ya na mana dadi. Tunda aka rantsar da shi bai guje wa mutane ba, a kullum burin sa shine me zai yi ya dadana wa talakan Bauchi rai.” Inji Haladu Mato.
Hotuna – Dahiru
Discussion about this post