Kungiyar Malaman Kwalejojin Kimiya da Fasaha ta Kasa (ASUP), ta yi barazanar tafiya yajin aiki matsawar gwamnatin tarayya ta kasa magance matsalolin da kungiyar ta nuna mata.
Ta bada wa’adi na kwanaki 21 ko dai a magance matsalolin ko kuma duk su tafi yajin aiki.
Kungiyar ta ce za ta fara lissafin wa’adin kwanaki 21 da ta bayar tun daga ranar 2 Ga Oktoba, domin gwamnati ta gaggauta nemo mafita daga dimbin matsalolin da suka dabaibaye ma’aikatan.
Dama tun cikin watan Nuwamba, 2017, sai da kungiyar ASUP ta tafi yajin aiki da nufin abin da ta kira nuna wa gwamnati yadda ta yi watsi da fannin ilmin fasaha a kasar nan.
Cikin wata takarda da kungiyar ta fitar a ranar Lahadi, Shugaban ASUP, Usman Dutse ya jaddada cewa kungiyar ta yanke shawarar yin haka ne domin ta sa gwamnatin tarayya aiwatar da alkawurran da ta dauka, wadanda ke kunshe a cikin yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma.
Ya kara da cewa gwamnati ta shafa musu mai a baki, ta yi musu alkawurra, wadanda a bisa hakan ne suka janye yajin aiki a cikin Nuwamba, 2017. Amma har yau ba a ma sake tuntubar su ba.
Ya lissafo kudaden alawus-alawus da dama wadanda aka hana malaman da sauran matsalolin da suka addabi malamai da kwalejojin wadanda a baya gwamnati ta yi alkawarin magance su.
A karshe ya ce daga yau sun daina yarda da duk wani badin baki da gwamnati za ta yi musu, domin ba cika alkawari za ta yi ba.