Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu, ya garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Ibadan, inda ya nemi kotun da yi masa cikakken bayanin fa’ida ko rashin fa’idar rashin zuwan sa aikin bautar kasa (NYSC), da bai yi ba, bayan kammala jami’a da ya yi.
Dama da PREMIUM TIMES ce ta fallasa rahoton cewa Shittu bai yi aikin bautar kasa bayan da ya kammala jami’a a digirin sa na farko ba.
An fallasa shi makonni biyu bayan saukar borin-kunya da tsohuwar Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ta yi, bayan da ita ma PREMIUM TIMES ta fallasa harkallar mallakar katin shaidar sahale mata aikin bautar kasa na jabu.
Yayin da Shittu ya ci gaba da zama a matsayin sa na minista, jam’iyyar sa ta APC kuma ta ki tantance shi fitowa daga cikin ’yan takarar gwamnan jihar Oyo a zaben 2019 mai zuwa.
Kamfanin DIllancin Labarai, NAN, ya ruwaito cewa Minista Shittu ya shigar da kara, a cikin wasikar da ya aika wa kotun mai lamba FCH/18/111/2018, inda a ciki ya ce ya na karar Shugaban Hukumar NYSC na Kasa da kuma na Jihar Oyo.
Shittu ya hada har da Ministan Shari’a da Gawamnatin Tarayya duk ya maka su kotu.
Abu na farko da ministan ya nema shi ne kotu ta hana wadanda ya kai karar su hudu tirsasa shi tafiya aikin bautar kasar da a baya bai yi ba.
Ya nemi kotu ta hana su tura shi aikin bautar kasa a yadda ya ke a yanzu godai-godai da shi.
Ya kuma roki ta hana wadanda ya kai kara din su dora masa wata tara, hukunci, kuma a hana su bayyana shi a matsayin tantirin mai laifi, don kawai bai je aikin bautar kasa ba.
Ba a nan Shittu ya tsaya ba. Ya kuma roki kotu ta umarci shugabannin NYSC na kasa, na jihar Oyo da Ministan Shari’a, su gaggauta damka masa takardar shaidar yin aikin bautar kasa, domin ya na gama digirin sa a fannin shari’a a jami’a, sai ya zarce ya zama dan majalisar jihar Oyo.
Shittu ya ce wannan wakilcin jama’a da ya yi a majalisar jihar Oyo, ai daidai ya ke da aikin bautar kasa.
Ko kuma ya ce a umarce su su damka masa takardar sahale masa aikin bautar kasa, ba sai ya je ba, domin zaman sa majalisar dokokin jihar Oyo bayan ya kammala Makarantar Koyon Shari’a, daidai ya ke da aikin bautar kasa.
Ya ce ya shiga majalisar dokokin jihar Oyo a zaben 1979, kuma yayin da ya bar majalisar a cikin 1983, shekarun sa sun haura 30 na ka’idar wanda aka yafe wa zuwa aikin bautar kasa.