Sanatan dake wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya yi tir da wani rahoto da jaridar Financial Times ta wallafa inda ta danganta wasu kalaman batanci ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari cewa shugaban Amurka Donald Trump ya yi a kan sa.
Shehu Sani ya bayyana cewa dole aja wa Trump kunne musamman ganin yadda baya daraja mutanen Afrika da ita kan ta nahiyar Afrika din.
” Irin kalaman da yayi amfani dasu kan shugaban kasa Muhammadu Buhari sam basu dace ba. Dole shugabannin kasashen Afrika su fito su nuna rashin jin dadin su ga irin haka sannan su maida masa martani da kakkausar murya.
A jiya Litinin ne jaridar Financial Times ta ruwaito cewa shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana ganawar da ya yi da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a matsayin marar wani tasiri ko tagomashi.
Haka jaridar Financial Times ta ruwaito cewa ganawar wadda suka yi cikin watan Afril, cewa ba ta da wani tasiri.
Cikin wata makala da jaridar ta buga, mai take, ‘Afrika na yi wa Trump kallon kitse a rogo,’ Financial Times a yau Litinin ta yi ikirarin cewa Trump ya shaida wa hadiman sa cewa shi fa ba da son ran sa ya karbi bakuncin shugaba maras tagomashi kamar shugaban Najeriya ba.
“Mutane uku ne suka tabbatar da cewa Trump ya furta haka,’’ kamar yadda jaridar ta yi ikirari.
Kakakin Yada Labaran Shugaban Kasa, Femi Adesina ya ki cewa komai, yayin da PREMIUM TIMES ta tuntube shi, don a ji ta bakin fadar shugaban kasa.
“Ni dai ba ni da ta cewa.” Inji Adesina.
Tuni ‘yan Najeriya har sun shiga shafukan twitter su na tofa albarkacin bakin su.

02254/30/4/2018//ICE/NAN
Mai shafin twitter @Veekid cewa ya yi, ai Trump mutum ne mai magana daya. Ya fadi abin da kowa ya sani game da Buhari.
“Ai na kalli taron manema labarai na hadin-guiwa da Trump ya yi shi da Buhari. Buhari har ya kammala bayani bai yi wata kwakkwarar magana ba tare da tangarda ba, kuma ya na magana ya kasa tsaida hankalin sa kan abin da ya kamata ya fada.”
Yayin da wasu ke goyon bayan Trump, wasu kuwa yabon Buhari suka yi, suka ce ya bai wa marada kunya.
Itama Jam’iyyar PDP ta tofa albarkacin bakin ta kan wannan magana da Trump ya yi inda ta ce irin maganganun da za a rika ji kenan idan har kasa ta zabi shugaban da bai cancanta ba duk da kadifirin da ya yi ta yi na neman amincewar shugabannin kasashen duniya.
Ana ta tsokacin kan furcin Trump, kungiyar Afenifere kira ta yi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya hakura da mulki hakanan ya je ya huta a 2019.