Gwamantin Tarayya ta tura tawagar gano musabbabin kashe-kashe a Zamfara

0

Cibiyar Wanzar da Zaman Lafiya da Sasanta Rikice-rikice, ta bayyana cewa za ta tura wata tawaga ta musamman zuwa jihar Zamfara, domin tantance musabbabin rikice-rikicen da suka dabaibaye jihar.

Daraktan-Janar na Rikon Cibiyar, Bakut T. Bakut, ya ce tunanin tura wannan tawaga ya bijiro ne, domin a samo mafita da kuma hanyar magance wannan mummunan kisan gilla da ake ta yi wa jama’a.

Bakut ya fadi haka ne a Abuja, ranar Talata, yayin da ya ke ganawa da manema labarai.

“A ranar 3 Ga Satumba mai zuwa, wannan cibiya za ta tura babbar tawaga zuwa Jihar Zamfara da sauran yankunan shiyyar, domin gano musabbabi da kuma irin wawakekiyar barnar da wannan rikici ya haifar. Sannan kuma za su bi domin su nemo hanyar ko hanyoyin da za a bi a kawo karshen wannan fitina.

“Za mu jajirce wajen yawan zaman tattaunawa da wadanda abin ya shafa a matakai na jiha, kananan hukumomi da unguwanni da matsuganai.”

Ya ce wannan gaggarimin aiki zai dauke su kamar makonni uku zuwa hudu ana gudanar da shi, yayin da za a mika sakamakon binciken ga gwamnatin tarayya, gwamnatin jiha da kuma bangarori na jami’ann tsaro.

Share.

game da Author