A yau litini ne shugaban hukumar hana yaduwar cutar kanjamau na kasa (NACA) Sani Aliyu ya bayyana cewa gwamnatocin jihohi a kasar nan na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen yaki da cutar.
Ya fadi haka ne a taron samun madafa game da bunkasa hanyoyin kula da masu fama da cutar ke samu a kasar nan da gidauniyar ‘AIDS Health Foundation (AHF)’ ta shirya a Abuja.
Aliyu ya bayyana cewa masu fama da cutar kanjamau na fama da rashin samun magunguna saboda tallafin da kasar ke samu daga kasashen waje ya fara raguwa.
” Sanin kowa ne cewa kashi 95 bisa 100 na kudaden da kasar ke samu na zuwa ne daga gwamnatin kasar Amurka da kungiyoyin bada tallafin na kasashen sai dai a yanzu wadannan kasashen sun fara janye tallafin da suke badawa.
Ya ce a yanzu haka bincike ya nuna cewa adadin yawan mutanen dake dauke da cutar kanjamau a Najeriya ya kai miliyan 3.4.
Ya ce Najeriya za ta iya kubuta daga wannan matsalar idan gwamnatocin jihohi da na tarayya sun fara ware kaso mai tsoka daga cikin kasafin kudin kasa a duk shekara.
Aliyu ya kuma ce gwamnati za ta kokarin hada hannu da kamfanonin sarrrafa magungun domin ganin an fara yin maganin cutar a kasa Najeriya maimakon shigowa da su da ake yi daga kasashen waje.
A karshe jam’in AHF Echey Ijezie, jam’iar UNAIDS Modupe Oduwole da shugaban kungiyar wayar da kan mutane kan cutar kanjamau (ACSAN), Nwakamma Ikenna sun koka cewa rashin ware isassun kudade da gwamnatin ke yi ne babbar matsalar da ake fama da shi a kasar nan.
Sun ce samar da isassun kudade ne zai sa a samu nasara kan wannan aiki da aka sa a gaba da wayar wa mutane cutar.
Discussion about this post